DARIQATIT TIJJANIYA

MUQAMAN DA ALLAH YA BAIWA ANNABI MUHAMMADU S.A.W. A RANAR HAIHUWA.


Lokacin Da Aka Haifi Annabi S.A.W. Allah Ya Mallaka Masa: Mabudan Taskokin Duniya Da Lahira.


Allah Ya Bashi Darajoji da Muqamai Na Annabi Adamu A.S.


Allah Ya Bashi Muqamai Da Ma’arifa Na Annabi Shisu A.S.


Allah Ya Bashi Sadaukantaka Na Annabi Nuhu A.S.


Allah Ya Bashi Muqamin Hulla Na Annabi Ibraheem A.S.


Allah Ya Bashi Yaren Larabci Da Muqamai Na Annabi Isma’il A.S.


Allah Ya Bashi Yardar Da Aka Ba Annabi Is'haqa A.S.

!

!Allah Ya Bashi Fasahar Annabi Salihu A.S. Da Muqamansa.

!

!

Allah ya Bashi Haquri da Muqamai Na Annabi Lu’du A.S.

!

!

Allah Ya Bashi Hikmar Annabi Luqman A.S.

!

!

Allah Ya Bashi Bisharorin Da aka ba Annabi Yaquba A.S.

!

!

Allah Ya bashi Kyawun Annabi Yusufa A.S.

!

!

Allah Ya Bashi Muqamai da Bin Allah Na Annabi Yunusa A.S.

!

!

Allah Ya Bashi Muqamai da Kwarjinin Annabi Yusha’u A.S.

!

!

Allah Ya Bashi Muqamai da Soyayya da Farin jinin Annabi Daniyal A.S.

!

!

Allah Ya Bashi Muqamai da Hukunci na Annabi Sulaiman A.S.

!

!

Allah Ya Bashi Muqamai da Dadin Murya Na Annabi Dawud A.S.

!

!

Allah Ya Bashi Muqamai da Natsuwa Na Annabi Ilyasu A.S.

!

!

Allah Ya Bashi Muqamai da Qabuli da kwarjini na Annabi Zakariyya’u A.S.

!

!

Allah Ya Bashi Muqamai da Isma Na Annabi Yahaya A.S. (Da Kiyayewa na zunubai).

!

!

Allah Ya Bashi Muqamai da Zuhudanci Na Annabi Isa A.S.

!

!

Allah Ya Bashi Dukkan Muqamai da Darajoji na Annabawa Sannan Ya Ninka ya Ninka Ya Ninka Ya Ninka Ya ninka Ya Ninka….. Akayita Ninka masa Ba Adadi SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM.


BISHARAR DA MANYAN ANNABAWA SUKAYI NA SAMUN CIKIN ANNABI MUHAMMADU S.A.W.

!

!

!

Watan Farko Wato Watan Rajab, Annabin da Ya Fara Zuwa Wajen Sayyida Amina A.S. Ya Gaida Annabi Kuma Yayi Mata Bishara Shine: ANNABI ADAMU A.S. Yazo Yana Haske Ya Kamshi Ya Duka a gabanta Yana cewa: “Barka Da zuwa Ya Shugabanmu Annabi Muhammadu S.A.W. Nazo ne In Gaisheka Kuma In Sallama maka Ya Rasullah”.

!

!

Sayyida Amina A.S. Tace Ban ganeka ba, Wanene kai? Sai Yace: Ai nine “Annabi Adamu Abul Bashar nazo ne inyi masa Muba’ya’a” Kuma Ina Yi miki Bishara cewa :”Kin Sami Cikin Shugaban Halittu Gaba Daya”.

!

!

Sayyida Amina Tace Annabi S.A.W. Yana Ciki amma Ya amsawa Annabi Adamu A.S. Sallama Kuma Ya Sanya Masa Albarka.

!

!

Kaji Wanda Annabawa ma suke Neman Albarkansa ANNABI MUHAMMADU S.A.W.

!

!

A WATA NA BIYU Watan Sha’aban ANNABI SHISU A.S. Sai Ga Wani Annabin Yana Haske Yana Kamshi Shima Ya duqa Gaba Sayyida Amina yace: “ASSALAMU ALAIKA YA RASULALLAH”.

!

!

Sayyida Amina A.S. Tace: “Ban Ganeka Ba” Sai Yace: "Ai nine Annabi Shisu A.S. Nazo ne inyi Muba’ya’a agareshi Kuma Inyi miki Bishara “Kin sami Cikin Mai Tawili Da Hadisi”.

!

!

Shima Yaji Muryar Annabi S.A.W. Ya Sanya Masa Albarka. Allah Kasa Annabi S.A.W. Yasanya Mana Albarka Da Wannan Maulidi Da Mukeyi.

!

!

WATA NA UKU Watan Ramadan Zuwan ANNABI IDRISU A.S.

!

!

Yazo Yana Haske Yana Kamshi Ya Duqa Gaban SayyidaAmina Yace:

“ASSALAMU ALAIKA YA NABIYULLAH”. Sayyida Amina A.S. Ta Tambayeshi Wanene Kai?. Sai Yace: "Nine Annabin Allah Annabi Idrisu nazo inyi miki Bishara Da Samun Wannan Ciki Mai Albarka Kuma Nazo ne In Sallama masa.

!

!

Kuma Ina yi miki bishara Kin Sami Cikin “LU’U LU’U MAI TSADA”.

!

!

“Ina Maki Bishara Domin Kin Sami Cikin”.

!

!

Annabi S.A.W. Ya Amsa Kuma Yasa Masa Albarka.

!

!

Allah Kayi mana Albarka Albarkacin Albarka shine Annabi Muhammadu S.A.W.

!

!

WATA NA HUDU Watan Shawwal ANNABI NUHU A.S. Ya sami Sayyida Amina A.S.Yana Kamshi Yana Haske Ya duqa yace: “ASSALAMU ALAIKA YA HABIBULLAH”.

!

!

Nazo ne In sallama maka Ya Rasullah, Kuma Ina Yi miki Bishara da cewa: “Kin sami Cikin Ma’abocin Nasara Da Fatahohi”.

!

!

Annabi S.A.W. Ya Amsa Kuma Ya Sanya Masa Albarka.

!

!

WATA NA BIYAR Watan Zul~Qada ANNABI HUDU A.S. Yana Haske Ya duqa a gaban Sayyida Amina A.S. Yace: “ASSALAMU ALAIKA YA SAFWATULLAH”.

!

!

Nazo ne nayi Muba’ya’a Kuma Inyi Miki Bishara cewa: “Lallai Kin sami Cikin Fiyayyen Duk Abin Haihuwa”.

!

!

Wadannan fa dukansu Annabawa ne

Kaji Yadda Suke Neman Fada wajen Annabi Muhammadu S.A.W. To Yaya Kai? Yaya Ni? Yaya Ke?.

!

!

WATA NA SHIDA WATAN ZUL~HAJJ Zuwan Annabi IBRAHIM A.S. Yazo Yana Haske Yana Kamsi Ya Duqa A Gaban Sayyida Amina A.S. Yace: “ASSALAMU ALAIKA RAHMATALLAH”.

!

!

Ya Gaishe Da Annabi S.A.W. Yayi Ma Sayida Amina A.S. Bishara da cewa: “Haqiqa Kin Sami Cikin Annabi Mai Girma”.

!

!

Annabi Ya Amsa masa ya sanya masa Albarka.

!

!

WATA NA BAKWAI Watan Al~Muharram Zuwan Annabi Isma'il A.S. Shima Yazo da kakkyawan Fuska Yana Haske Ya Gaida Annabi S.A.W. Yace: “ASSALAMU ALAIKA YA MANIKHTARAHULLAH”.

!

!

Yace Nine Annabi Isma’il A.S. Nazo in gaida shugaba kuma Inyi miki Bishara cewa: “Kin Sami cikin Ma’abocin Falala Ingantacce”.

!

!

Annabi S.A.W. Ya Amsa Kuma Ya Sanya Masa Albarka.

!

!

WATA NA TAKWAS Watan Safar ANNABI MUSA A.S.

!

!

Yayi Sallama Yana Gaida Annabi Yana cewa: "ASSALAMU ALAIKA YA HIRATULLAH". Yace mata Nine Annabin Allah Annabi Musa A.S. Nazo ne Domin In Miki Bishara cewa: “Hakika Kin Sami Cikin Wanda Allah Zai Bashi Alqur’ani Mai Girma".

!

!

"LA'ILAHA ILLALLAH" SAURA WATA DAYA ANNABI S.A.W. YA ZO DUNIYA A SHARI'A KENAN.

!

!

WATA NA TARA WATAN RABI’UL AWWAL Zuwan ANNABI ISAH A.S. {Rahillahi}. Ku sani Fa A Wannan Wata ne Daren Sha Biyu Ga Wata Daren Litini Annabi Muhammadu S.A.W. Ya Sauka A Duniya.

!

!

Sayyida Amina A.S. Taga Wannan Bako Yazo Yana Haske Yana Qamshi. Ya duqa yace: “ASSALAMU ALAIKA YA RASULALLAH”.

!

!

Yace mata Nazo ne inyi maki Bishara domin kin sami cikin “Annabin Allah abin karramawa abin Girmamawa”.

!

!

Annabi Muhammadu S.A.W. Yasanya Masa Albarka Tun Yana Ciki.

!

!

Kaji Dai Yadda Ake Neman Fada A Wajen Annabi Muhammadu S.A.W.

!

!

Don Allah Idan Ka Karanta Wannan Kayi Salatil Fatihi Kafa Daya Ga Annabi S.A.W.

!

!

ALLAHUMMA SALLI ALA SAYYIDINA MUHAMMADIN WA ALA ALIHI HAQQA QADRIHI WA MIQDARIHIL AZEEM.

Make a free website with Yola