BISHARAR DA MANYAN ANNABAWA SUKAYI NA SAMUN CIKIN ANNABI MUHAMMADU S.A.W.
Watan Farko Wato Watan Rajab, Annabin da Ya Fara Zuwa Wajen Sayyida Amina A.S. Ya Gaida Annabi Kuma Yayi Mata Bishara Shine: ANNABI ADAMU A.S. Yazo Yana Haske Ya Kamshi Ya Duka a gabanta Yana cewa: “Barka Da zuwa Ya Shugabanmu Annabi Muhammadu S.A.W. Nazo ne In Gaisheka Kuma In Sallama maka Ya Rasullah”.
Sayyida Amina A.S. Tace Ban ganeka ba, Wanene kai? Sai Yace: Ai nine “Annabi Adamu Abul Bashar nazo ne inyi masa Muba’ya’a” Kuma Ina Yi miki Bishara cewa :”Kin Sami Cikin Shugaban Halittu Gaba Daya”.
Sayyida Amina Tace Annabi S.A.W. Yana Ciki amma Ya amsawa Annabi Adamu A.S. Sallama Kuma Ya Sanya Masa Albarka.
Kaji Wanda Annabawa ma suke Neman Albarkansa ANNABI MUHAMMADU S.A.W.
A WATA NA BIYU Watan Sha’aban ANNABI SHISU A.S. Sai Ga Wani Annabin Yana Haske Yana Kamshi Shima Ya duqa Gaba Sayyida Amina yace: “ASSALAMU ALAIKA YA RASULALLAH”.
Sayyida Amina A.S. Tace: “Ban Ganeka Ba” Sai Yace: "Ai nine Annabi Shisu A.S. Nazo ne inyi Muba’ya’a agareshi Kuma Inyi miki Bishara “Kin sami Cikin Mai Tawili Da Hadisi”.
Shima Yaji Muryar Annabi S.A.W. Ya Sanya Masa Albarka. Allah Kasa Annabi S.A.W. Yasanya Mana Albarka Da Wannan Maulidi Da Mukeyi.
WATA NA UKU Watan Ramadan Zuwan ANNABI IDRISU A.S.
Yazo Yana Haske Yana Kamshi Ya Duqa Gaban SayyidaAmina Yace:
“ASSALAMU ALAIKA YA NABIYULLAH”. Sayyida Amina A.S. Ta Tambayeshi Wanene Kai?. Sai Yace: "Nine Annabin Allah Annabi Idrisu nazo inyi miki Bishara Da Samun Wannan Ciki Mai Albarka Kuma Nazo ne In Sallama masa.
Kuma Ina yi miki bishara Kin Sami Cikin “LU’U LU’U MAI TSADA”.
“Ina Maki Bishara Domin Kin Sami Cikin”.
Annabi S.A.W. Ya Amsa Kuma Yasa Masa Albarka.
Allah Kayi mana Albarka Albarkacin Albarka shine Annabi Muhammadu S.A.W.
WATA NA HUDU Watan Shawwal ANNABI NUHU A.S. Ya sami Sayyida Amina A.S.Yana Kamshi Yana Haske Ya duqa yace: “ASSALAMU ALAIKA YA HABIBULLAH”.
Nazo ne In sallama maka Ya Rasullah, Kuma Ina Yi miki Bishara da cewa: “Kin sami Cikin Ma’abocin Nasara Da Fatahohi”.
Annabi S.A.W. Ya Amsa Kuma Ya Sanya Masa Albarka.
WATA NA BIYAR Watan Zul~Qada ANNABI HUDU A.S. Yana Haske Ya duqa a gaban Sayyida Amina A.S. Yace: “ASSALAMU ALAIKA YA SAFWATULLAH”.
Nazo ne nayi Muba’ya’a Kuma Inyi Miki Bishara cewa: “Lallai Kin sami Cikin Fiyayyen Duk Abin Haihuwa”.
Wadannan fa dukansu Annabawa ne
Kaji Yadda Suke Neman Fada wajen Annabi Muhammadu S.A.W. To Yaya Kai? Yaya Ni? Yaya Ke?.
WATA NA SHIDA WATAN ZUL~HAJJ Zuwan Annabi IBRAHIM A.S. Yazo Yana Haske Yana Kamsi Ya Duqa A Gaban Sayyida Amina A.S. Yace: “ASSALAMU ALAIKA RAHMATALLAH”.
Ya Gaishe Da Annabi S.A.W. Yayi Ma Sayida Amina A.S. Bishara da cewa: “Haqiqa Kin Sami Cikin Annabi Mai Girma”.
Annabi Ya Amsa masa ya sanya masa Albarka.
WATA NA BAKWAI Watan Al~Muharram Zuwan Annabi Isma'il A.S. Shima Yazo da kakkyawan Fuska Yana Haske Ya Gaida Annabi S.A.W. Yace: “ASSALAMU ALAIKA YA MANIKHTARAHULLAH”.
Yace Nine Annabi Isma’il A.S. Nazo in gaida shugaba kuma Inyi miki Bishara cewa: “Kin Sami cikin Ma’abocin Falala Ingantacce”.
Annabi S.A.W. Ya Amsa Kuma Ya Sanya Masa Albarka.
WATA NA TAKWAS Watan Safar ANNABI MUSA A.S.
Yayi Sallama Yana Gaida Annabi Yana cewa: "ASSALAMU ALAIKA YA HIRATULLAH". Yace mata Nine Annabin Allah Annabi Musa A.S. Nazo ne Domin In Miki Bishara cewa: “Hakika Kin Sami Cikin Wanda Allah Zai Bashi Alqur’ani Mai Girma".
"LA'ILAHA ILLALLAH" SAURA WATA DAYA ANNABI S.A.W. YA ZO DUNIYA A SHARI'A KENAN.
WATA NA TARA WATAN RABI’UL AWWAL Zuwan ANNABI ISAH A.S. {Rahillahi}. Ku sani Fa A Wannan Wata ne Daren Sha Biyu Ga Wata Daren Litini Annabi Muhammadu S.A.W. Ya Sauka A Duniya.
Sayyida Amina A.S. Taga Wannan Bako Yazo Yana Haske Yana Qamshi. Ya duqa yace: “ASSALAMU ALAIKA YA RASULALLAH”.
Yace mata Nazo ne inyi maki Bishara domin kin sami cikin “Annabin Allah abin karramawa abin Girmamawa”.
Annabi Muhammadu S.A.W. Yasanya Masa Albarka Tun Yana Ciki.
Kaji Dai Yadda Ake Neman Fada A Wajen Annabi Muhammadu S.A.W.
Don Allah Idan Ka Karanta Wannan Kayi Salatil Fatihi Kafa Daya Ga Annabi S.A.W.
ALLAHUMMA SALLI ALA SAYYIDINA MUHAMMADIN WA ALA ALIHI HAQQA QADRIHI WA MIQDARIHIL AZEEM
KA'ABU YAYI BISHARAR ZUWAN ANNABI MUHAMMADU S.A.W.
Sayyidina Ka’abu Yana Daga Cikin Kakannin Annabi Muhammadu S.A.W.
Ya Kasance Duk Ranar Juma’a Yana Tara Mutane Yana Basu Bayanai akan Annabin Karshen Zamani.
Har yakanyi masu Ishara da cewa Acikin su ne Allah zai bayyanar dashi.
Sun Kasance Tun a wancan Lokacin suna Tawassuli Da Annabi Muhammadu S.A.W
BISHARORI NA ZUWAN ANNABI MUHAMMADU S.A.W. DAGA MANYAN BOKAYEN YAHUDAWA.
A Garin Yamama akwai wasu Manyan Bokaye Wadanda a lokacin indai Bokanci ne babu kamarsu a duniya, Kuma Dukansu sunyi Bayanin Zuwan Annabi S.A.W. Da Sufofinsa fiye da Tinaninka, Ga Bayanin Daya Daga Cikin Bokayen.
BOKA NA FARKO SUNANSA SADIHU:- Wannan Sadihun Babban Boka ne Masanin Taurari awannan Lokacin, Shi wani Irin Halitta ne domin bashi da Hannu Bashi Da Kafa, daga Kai Sai Jiki: Dakko shi akeyi a kwanon kaya, Amma Sai Ilimi.
Wata Rana Ya Fito da daddare Yana Duba Taurari, Sai Yaga Sun Hargitse(Sai Ya Gane cewa Lallai Ba Lafiya ba) domin Yasan cewa Hakan Kawai zai iya Faruwa ne idan Har an sami cikin Annabin Karshen Zamani, Domin Shine zai zo da Addinin Musulunci zai hana Bokanci.
Sai Ya Rubuta Wasika Zuwa ga babbar Boka Ta Mace Wacce itama a duniya babu kamarta wajen ilimin Taurari da Bokanci Sunanta Zarqa’u (Bayanin ta zai zo a rubutu na gaba da izinin Allah).
Yace mata: “Lallai yaga Taurari sun rikice, kuma wannan yana nuna Alamar Bayyanan wannan Annabin Mai hallaka kafirai, mai dusashe duk addinan karya, wanda zai Zubar da jinane na kafirai Annabin Karshen Zamani, Kuma Na Tabbatar Zai Bayyana Ne a Garin Makka, Nima daga Nan Garin Makka Zan tafi domin in Tabbatar da hakan Mu Hadu dake A can”.
Aka Daukeshi zuwa Garin Makka, Yayita Bayanin Sufofin Annabi S.A.W. Kuma Har Ya Nuna Ma Mutanen Makka Cewa Ga Mahaifiyar Annabi S.A.W. Da Mahifiyar Sayyiduna Aliyu.
Banu Abdu Munafin Sunata Farin ciki domin acikin su ne, Amma Yahudawa Sukayi Bakin ciki da jin Wannan Labari.
Sadihu Ya Sami Kwanaki A Garin Makka Yana Basu Bayanin Sufofin Annabi Muhammadu S.A.W.
Abin Nufi Anan Shine Fassarar Ayannar Na cikin Suratul Bakara da Allah Yake cewa:
ﻳﻌﺮﻓﻮﻣﻪ ﻛﻤﺎ ﻳﻌﺮﻓﻮﻥ ﺍﺑﻨﺎﺀﻫﻢ
Cewa su Yahudawan nan Sun San Annabi S.A.W. Kamar Yadda Suka san 'Ya'yan Cikinsu, wasu ma sun sanshi fiye da 'Ya'yan cikinsu” amma duka bai sanya Sunyi Imani ba.
Akwai Cikakken Bayanin da Kisaa na “SADIHU” A karatun Da Maulana Sheikh Usman Kusfa Zaria R.A. Yayi Na Tarihin Annabi S.A.W. (04).