learn more..................


MENENE AZUMI
Azumi na nufin; kamewa ga barin wani abu
Amma a shari'a (الصَّوْمُ) assaumu shi ne kamewa ga barin ci da sha da barin yin jima’i tun daga bullowar alfijir har zuwa faduwar rana da niyyar yin ibada ga Allah.
Ubangiji madaukakin Sarki yana cewa:
قَالَ تَعَالَى: "يَأَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا كُتِبَ عَلَيْكُمُ الصِّيَامُ كَمَا كُتِبَ عَلَى الَّذِينَ مِنْ قَبْلِكُمْ لَعَلَّكُمْ تَتَّقُونَ." (سورة البقرة: 183)
Ma'ana: “Ya ku wadanda kuka yi imani, hakika, an wajabta muku yin Azumi kamar yadda aka wajabta (shi) ga wadanda suka gabace ku domin ku ji tsoron Allah.” (Al- Bakara: 183).
Sannan Manzon Allah (S.A.W) ya ce:
"بني الإسلام على خمس شهادة أن لا إلـه إلا الله وأن محمدا رسول الله وإقام الصلوة وإيتاء الزكاة وحج البيت وصوم رمضان" رواه البخاري ومسلم.
“An gina Musulunci a bisa abubuwa guda biyar; shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma Annabi Muhammad (S.A.W) Manzon Allah ne, da tsai da Salla da ba da Zakka da ziyartar Dakin Allah (Aikin Hajji) da azumtar watan Ramadan” (Bukhari da Muslim).
Azumin watan Ramadan rukuni ne daga cikin rukunan Musulunci guda biyar. Kuma Ubangiji Madaukakin Sarki ya wajabta wa wannan al’umma azumtar watan Ramadan.
Hakika, an wajabta azumtar watan Ramadan a cikin shekara ta biyu daga hijirar Manzon Allah (S.A.W) daga Makkah zuwa Madina.

RABE-RABEN AZUMI:
Azumi ya kasu izuwa kaso biyu:
- Azumin Farilla wato na Wajibi.
- Da kuma Azumi na Nafila:
Azumin Farilla su ne:
- Azumin Watan Ramadan.
- Azumin Kaffara (Ramuwa).
- Azumin Bakance (Yin Alkawari).
Azumin Nafila su ne:
- Azumin Kwanaki shida a cikin Watan Shawwal.
- Azumin ranar Arfa ga wanda bai je aikin Hajji ba.
- Azumin Watan Muharram, Ashura da watanta.
- Azumin Litinin da Alhamis.
- Azumin kwanaki uku a cikin kowanne wata.
Da sauransu.


FALALAR AZUMIN RAMADAN
Hakika, Azumin watan Ramadan yana da lada mai girma, kuma yin ibada a cikinsa tana da falala mai yawa wacce ta fi ta sauran watanni.
Hadisai da yawa sun fadi falalar Azumin Ramadan. Daga cikin Hadisai akwai:
قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: "إِذَا جَاءَ رَمَضَانُ فُتِحَتْ أَبْوَابُ الْجَنَّةِ وَغُلِقَتْ أَبْوَابُ الْنِيرَانِ وَصُفِّدَتِ الشَّيَاطِينَ." (رواه البخارى)
Ma'ana:
Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Idan watan Azumin Ramadan ya zo, ana bude kofofin Aljanna, kuma ana rufe kofofin wuta, kuma ana daure shaidanu.” (Bukhari ne ya rawaito).
عَنْ أَبِى سَعِيدِ الْخُدْرِى رَضِيَ اللهُ عَنْهُ أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: "مَا مِنْ عَبْدٍ يَصُومُ يَوْمًا فِي سَبِيلِ اللهِ إِلاَّ بَاعَدَ اللهُ بِذَلِكَ عَنِ النَّارِ سَبْعِينَ خَرِيفًا." (رواه البخارى ومسلم)
Ma'ana:
An karbo daga Abi Sa’idil Khudri (R.A) ya ce, Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Babu wani bawa da zai azumci rana daya saboda Allah face sai Allah ya nisanta fuskarsa ga barin wuta shekara saba’in.” (Bukhari da Muslim ne suka rawaito).
عَنْ أَبِى هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللهُ عَنْهُ أَنَّ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: مَنْ صَامَ رَمَضَانَ إِيمَانًا وَاحْتِسَابًا غُفِرَ لَهُ مَا تَقَدَّمَ مِنْ ذَنبِهِ." (رواه أحمد)
Ma'ana:
An karbo daga Abu Huraira (R.A) ya ce, Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Duk wanda ya azumci watan Ramadan yana mai imani da neman lada za a gafarta masa abin da ya gabatar daga zunubinsa.” (Ahmad ne ya rawaito).

Hakika, Allah Madaukakin Sarki ya yi alkawari gwaggwaba, sakamako ga wanda ya azumci watan Ramadan.
Sannan Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Duk aikin alherin da dan’adam ya yi Allah yana ninka masa lada goma har zuwa dari bakwai. Allah (S.W.T) yana cewa, sai dai Azumi, shi nawa ne, ni ake yi wa, kuma ni zan ba da sakamakon yin sa. Domin mai Azumi yana da farin ciki guda biyu, farin cikin farko lokacin da zai yi buda baki, na biyu kuma lokacin da zai gamu da Ubangijinsa, hakika, warin bakin mai Azumi ya fi turaren almiski kamshi a wajen Allah.” (Muslim ne ya rawaito).
Da sauransu da dama.


HUKUNCIN KIN YIN AZUMIN RAMADAN
Duk wanda ya ci abinci da rana da gangan a cikin watan Ramadan ba tare da wani uzuri da shari’a ta halatta ba, babu shakka azabar da za a yi masa mai tsanani ce. Kuma ko da zai mutu yana Azumi ba zai zama ya cike wannan ranar da ya ci ba.
عَنْ أَبِى هُرَيْرَةَ رَضِيَ الله عَنْهُ أَنَّ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: "مَنْ أَفْطَرَ يَوْمًا فِي رَمَضَانَ فِي غَيْرِ رُخْصَة رَخَّصَهَا الله لَهُ، لَمْ يَقْضِ عَنْهُ صِيَامَ الدَّهْرِ كُلِّهِ وَإِنْ صَامِهُ." (رواه أبو داود وابن ماجه، والترمذى)
Abu Huraira (R.A) ya ce, Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Wanda ya ci abinci a rana daya daga cikin ranakun Ramadan ba tare da wani sauki da Allah ya yi masa ba, to, ku da zai azumci baki dayan zamaninsa bai rama ba.” (Abu Dauda da Ibn Majah da Tirmizi).


YAUSHE AKE AZUMIN WATAN RAMADAN
Yin Azumin watan Ramadan yana wajaba da dayan abubuwa guda biyu:
1. Ganin watan Ramadan
قَالَ الله تَعَالَى: "فَمَنْ شَهِدَ مِنْكُمُ الشَّهْرَ فَلْيَصُمْهُ." (البقرة: 185)
“Duk wanda ya tabbatar da tsayuwar watan to ya azumce shi.” (Al Bakara: 185).
Idan mutum ya ga watan Ramadan shi kadai, kuma shi mutumin adali ne, wanda aka aminta da adalarsa, to, za a yi aiki da maganarsa ta ganin wata a wajen mafi yawancin ma’abota ilimi.”
عَنِ ابْنِ عُمَرَ رَضِيَ الله عَنْهُ قَالَ: تَرَاى النَّاس الْهِلاَل فَرَأَيْتَهُ، فَأَخْبَرْتُ رَسُولُ اللهِ صَلَّى الله عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَصَامَ وَأَمَرَ النَّاس بِصِيَامه." (رواه أبو داود).
Don fadin Abdullahi ibn Umar (R.A) ya ce: “Mutane sun ga wata, kuma ni ma na gan shi, don haka, sai na je na ba wa Manzon Allah (S.A.W) labari, sai (Annabi) ya yi Azumi, kuma ya umarci mutane su ma su azumta.” (Abu Dawud ne ya rawaito).

2. Cikar Watan Sha’aban Kwana Talatin
Idan sama ta yi duhu gajimare ya rufe ta a ranar ashirin da tara ba a ga wata ba har aka wayi gari ranar talatin ga wata, to, wajibi ne a ranar talatin kowa ya dauki Azumi.
لِحَدِيثِ ابْنِ عُمَر رَضِيَ اللهُ أَنَّ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: "الشَّهْرُ تِسْعَ وَعِشْرُونَ لَيْلَةً، فَلاَ تَصُومُوا حَتَّى تَرَوْهُ، فَإِنْ غُمَّ عَلَيْكُمْ فَأَكْمِلُوا الْعِدَّةَ ثَلاَثِينَ." (رواه البخارى).
Saboda hadisin Abdullahi dan Umar (R.A) inda ya ce, Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Wata dare ashirin da tara ne (don haka) kar ku yi Azumi har sai kun ga wata, idan kuwa sama ta yi girgije, to, sai ku lissafa kwana talatin.” (Bukhari ne ya rawaito).


A KAN WA AZUMIN RAMADAN YA WAJABA?
Azumin watan Ramadan yana wajaba a kan dukkan Musulmi mai hankali baligi wanda zai iya yin Azumin ba tare da wata matsananciyar wahala ba.


SU WA AKA YARDA SU JINKIRTA:
Me haila da nifasi da mara lafiya da mai shayarwa ko mai cikin da zasu galabaita ko abin shayarwarsu, da matafiyi a tafiyar da ba ta sabo ba wadda ta zarce nisan kilo-mita (80), suna da rangwame, sai su kirga kwanakin da suka sha, bayan Ramadan sai su rama.



RUKUNAN AZUMI
Amma rukunan Azumi guda biyu ne:
1. Niyya:
Azumi ba ya yiwuwa idan babu niyya,
لِقَوْلِهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: "إنما الأعمال بالنيات" (رواه البخاري ومسلم)
“Dukkanin ayyuka basa yiwuwa sai da niyya.” (Bukhari da Muslim).
Da mutum zai dauki niyyar Azumin watan Ramadan a daren da ake zaton ganin wata ya kwanta bacci da niyyar idan an ga wata zai yi Azumi, idan kuwa ba a gani ba, zai ci gaba da cin abincinsa, sai aka ga wata yana bacci. Da gari ya waye, sai ya tashi bai ci abinci ba, bai yi abin da yake bata Azumi ba, sai aka gaya masa jiya yana bacci an ga wata, to wajibi ne ya kame bakinsa, kuma bayan Salla ya rama Azumi daya.
لِقَوْلِهِ عَمَّرُ ابْنِ يَاسِرٍ رَضِيَ الله عَنْهُ: "مَنْ صَامَ الْيَوْمَ الَّذِى يُشَكُّ فِيهِ فَقَدْ عَصَى أَبَا الْقَاسِمُ."
2. Kamewa ga barin ci da sha
Rukuni na biyu daga cikin rukunan Azumi shi ne kamewa ga barin duk wani abinci ko abin sha ko jima’i.
لِقَوْلِهِ تَعَالَى: "وَكُلُوا وَاشْرَبُوا حَتَّى يَتَبَيَّنَ لَكُمُ الْخَيْطِ اْلأَبْيَضِ مِنَ الْخَيْطِ اْلأَسْوَدِ مِنَ الْفَجْرِ ثُمَّ أَتِمُّوا الصِّيَامَ إِلَى اللَّيْلِ." (سورة البقرة: آية 187)
Ma'ana:
“Ku ci ku sha har izuwa ku bambance tsakanin farin zare da bakin zare daga hasken alfijir, sannan ku cika Azumi izuwa dare.” (Suratul Bakara: aya ta 187).


SUNNONIN AZUMI DA LADUBBANSA
Azumi yana da sunnoni da mustahabbai, yaa daga cikinsu:
1. Sahur: shi mustahabbi ne a gamuwar malamai, wanda bai yi shi ba ba shi da lafi sai dai wanda ya yi sahur ya fi shi yawan lada. Domin Annabi (S.A.W) ya yi umarni da a yi shi.
عَنْ أَنَسٍ رَضِيَ اللهُ عَنْهُ أَنَّ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: "سَحَّرُوا فَإِنَّ فِي السُّحُورِ بَرَكَةٌ." (رواه البخارى ومسلم).
An karbo daga Anas dan Malik (R.A) ya ce, Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Ku yi sahur hakika, akwai albarka a cikin yin sahur.” (Bukhari da Muslim ne suka rawaito).
2. Gaggauta yin buda baki da jinkirta sahur.
لِقَوْلِ النِّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: "لاَ يَزَالُ النَّاسُ بِخَيْرٍ مَا عَجَّلُوا الْفِطْرَ وَأَخّرُوا السُّحُورَ." (رواه البخارى ومسلم)
Don fadin Annabi (S.A.W) da ya ce: “Mutane ba za su gushe suna cikin alheri ba, muddin suna gaggauta buda baki kuma suna jinkirta sahur.” (Bukhari da Muslim ne suka rawaito).
3. Yin buda baki da dabino:
لِقَوْلِهِ عَلَيْهِ الصَّلاَةُ وَالسَّلاَمُ: "إِذَا أَفْطَرَ أَحَدُكُمْ فَلْيَفْطِرُ عَلَى تَمْرٍ فَإِنَّهُ بَرَكَةً فَإِنْ لَمْ يَجِدْ تَمْرًا فَالْمَاءُ فَإِنَّهُ طَهُورٌ." (رواه أبو داود والترمذى)
Don fadin Manzon Allah (S.A.W) da ya ce: “Idan dayanku zai yi buda baki ya yi buda baki da dabino, idan bai samu dabino ba, ya yi da ruwa, don tsarki ne ko tsarkakakke ne.” (Abu Dawud da Tirmizi ne suka rawaito).
4. Addu’a yayin buda baki:
عَنْ عَبْدِ اللهِ ابْنِ عُمَرُو بْنِ الْعَاص: أَنَّ النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: "إِنَّ لِلصَّائِمِ عِنْدَ فِطْرِهِ دَعَوَةٌ مَا تُرَد." (رواه ابن ماجه).
An karbo daga Abdullahi dan Amru dan As (R.A) ya ce Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Hakika, mai Azumi in ya yi addu’a lokacin buda baki ba a mayar da addu’ar (ana amsawa).” (Dan Maja ne ya rawaito).
Annabi (S.A.W) ya kasance idan zai yi buda baki yana cewa:
"اللَّهُمَّ لَكَ صُمْنَا وَعَلَى رِزْقِكَ أَفْطَرْنَا فَتَقَبَّلْ مِنَّا إِنَّكَ أَنْتَ السَّمِيعُ الْعَلِيمُ" (أبو داود)
Ma’ana: “Ya Ubangiji dominKa muka yi Azumi, kuma da arzikinKa muke buda baki, ka karba daga gare mu, lallai Kai mai ji ne Masani.” (Abu Dawuda ne ya rawaito).
Da wasu addu'o'in da dama.
5. Asuwaki: An so ga mai Azumi ya yi asuwaki lokacin azuminsa.
Saboda Manzon Allah (S.A.W) ya kasance yana yin asuwaki lokacin da yake Azumi.
Hakanan yana daga ladubban Azumi a nisanci shaidar zur, karya, giba, rada, tashin hankali, da dai sauran ayyukan sabo.


ME KE HALATTA GA MAI AZUMI
1. Hakika, Allah Madaukakin Sarki ya yi wa Musulmi sauki lokacin Azumi da daddare su sadu da iyalansu.
قَالَ تَعَالَى: "أُحِلَّ لَكُمْ لَيْلَةَ الصِّيَامِ الرَّفَثُ إِلَى نَسَائِكُمْ." (سورة البقرة: 187 آية)
Ma'ana: Ubangiji Madaukakin Sarki ya ce: “An halasta gare ku a daren Azumi ku kusanci matanku.” (Suratul Bakara: aya ta 187).
An karbo daga Barra’u ya ce, yayin da Allah (S.W.T) ya wajabta Azumin Ramadan, sahabbai sun kasance ba sa saduwa da iyalansu da daddare, har sai da Allah ya saukar da wannan ayar.

2. Babu laifi mai Azumi ya wayi gari da janaba a cikin watan Ramadan.
عَنْ عَائِشَةَ وَأُمُّ سَلَمَة رَضِيَ اللهُ عَنْهُمَا: "أَنَّ رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ كَانَ يُدْرِكُهُ الْفَجَرَ وَهُوَ جُنُبٌ مِنْ أَهْلِهِ ثُمَّ يَغْتَسِلُ وَيَصُومُ." (رواه البخارى)
An karbo daga Aisha da Ummu-Salama (R.A) suka ce, Manzon Allah (S.A.W) ya kasance alfijir yana riskarsa yana mai janabar saduwa da iyalansa, sannan ya yi wanka kuma ya yi Azumi. (Bukhari ne ya rawaito).
Abu Dawud ya rawaito Hadisi daga Nana Aisha (R.A) ya ce, ta ce, Manzon Allah (S.A.W) ya kasance yana runguma ta lokacin da yake Azumi kuma ni ma ina Azumi. (Abu Dawud).
Idan mutum ya sumbaci matarsa ko ya rungume ta har ya fitar da maziyi to ba komai a gare shi.
Idan kuma mutum ya rungumi matarsa ko ya sumbace ta, lokacin duk suna Azumi har dayansu ya zubar da maniyi to Azumin wanda ya zubar da maniyyin ya baci kuma sai ya rama Azumi.
3. Yin Kaho: Idan mutum yana Azumi sai ya sa aka yi masa kaho, shi ma ba komai a gare shi.
عَنِ ابْنِ عَبَّاسٍ رَضِيَ اللهُ عَنْهُ قَالَ: "احْتَجَمَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ وَهُوَ صَائِمٌ." (رواه البخارى)
An karbo daga dan Abbas (R.A) ya ce, Manzon Allah (S.A.W) ya yi kaho a lokacin da yake Azumi. (Bukhari ne ya rawaito).
4. Sa Kwalli: Anas dan Malik (R.A) ya kasance yana sa kwalli lokacin da yake Azumi.


HUKUNCIN MAI AZUMIN DA YA CI ABINCI DA MANTUWA
Idan mutum yana Azumi sai ya ci ko ya sha abin sha da mantuwa, azuminsa ingantacce ne, babu ramuwa a gare shi bare kaffara.
عَنْ أَبِى هُرَيْرَةَ رَضِيَ اللهُ عَنْهُ أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: "مَنْ نَسِىَ وَهُو صَائِمٌ فَأَكَلَ أَوْ شَرَبَ فَلْيَتِمَّ صَوْمَهُ فَإِنَّمَا أَطْعَمَهُ الله وَسَقَاهُ." (رواه البخارى)
An karbo daga Abu Huraira (R.A) ya ce, Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Wanda ya manta ya ci ko ya sha lokacin da yake Azumi, to, ya ci gaba da azuminsa, hakika, Allah ne ya ci da shi ya shayar da shi.” (Bukhari ne ya rawaito)
Idan mutum yana Azumi sai amai ya zo masa ya amayar to, babu komai a gare shi.
Don fadin Manzon Allah (S.A.W) da ya ce: “Wanda amai ya zo masa (lokacin yana Azumi) ya amayar ba komai a gare shi, idan kuwa da gangan ya jawo aman to, ya rama Azumi.” (Tirmizi ne ya rawaito).


ME KE BATA AZUMI
- Ridda, wato fita daga Musulunci.
- Ci ko sha da gangan ba tare da uzuri ba.
- Haila ko Nifasi, sai dai a kirga kwanakin da aka sha a rama su bayan Ramadan.
- Jima'i, Tarawa da mutum ko dabba ko ma da menene.
- Fitar maniyyi dan sha'awa ko da jima'i ko babu.
- Kakaro amai da gangan.
- Hauka.
Da sauransu.
Idan namiji da mace zuka sadu da rana a cikin watan Azumi to, azuminsu ya baci, sai su rama kuma su yi kaffara.
Don fadin Abu Huraira (R.A) ya ce, wata rana Manzon Allah (S.A.W) yana zaune sai wan mutum ya zo ya ce, ya Rasulullahi, na halaka, sai Annabi ya ce da shi, mai ya halaka ka? Sai ya ce, na sadu da matata a cikin watan Azumi da rana, sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce da shi, za ka sami abin da za ka ’yanta bawa? Sai ya ce, a’a, sai ya ce, za ka iya yin Azumi watanni biyu a jere? Sai ya ce, a’a, sai ya ce, shin za ka sami abin da za ka ciyar da miskinai sittin? Sai ya ce, a’a, sai mutumin ya zauna a wajen Annabi har aka kawo wa Annabi buhun dabino. Sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce da shi, dauki ka yi sadaka da shi, sai ya ce, ai duk cikin Madina babu wanda ya fi ne bukata. Sai Manzon Allah (S.A.W) ya yi dariya har sai da hakoransa suka bayyana. Sannan ya ce, dauki ka je ka ciyar da iyalanka.” (Jama’a da yawa ne suka rawaito).



RANAKUN DA AKA HANA AZUMIN NAFILA
- Ranakun Idi guda biyu, wato ranar karamar sallah da babbar sallah.
- Hakanan kwanakin ukun da ke gaban ranar babbar sallah (Ayyamut tashrik) sai da uzuri.
- Kebantar ranar Juma'a kawai, sai dai ka hada ta gabanta ko ta bayanta.
- Kebantar ranar Asabar kawai, sai dai ka hada gabanta ko ta bayanta.
- Hakanan ranar shakku, kamar ana zaton gobe Ramadan zai kama ko kuwa.
- Hakanan yin Azumi katutur ba hutawa kullum.
- Hakanan matar da mijinta yake nan a gari sai da izininsa.
- Hakanan jeranta azumi ba tare sahur ko buda baki ba, ayi kwanaki ana haka.

I'ITIKAFI
Ma’anar li’itikafi shi ne lazimtar Masallaci da zama a cikinsa da niyyar neman kusanci da Allah Tabaraka wa Ta’ala.
Hukuncinsa: Shi li’itikafi sunna ce mai karfi, kuma a goman karshe na watan Ramadan ake yin sa. Amma yin sa a wani watan mustahabbi ne.
"فَقَدْ كَانَ النَّبِي صَلَّى الله عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَعْتَكِفُ فِي كُلِّ رَمَضَانَ عَشَرَةَ أَيَّامٍ، فَلَمَّا كَانَ الْعَامَ الَّذِى قُبِضَ فِيهِ اعْتِكَفَ عِشْرُونَ يَوْمًا. (رواه البخارى)
Ma'ana:
Hakika, Manzon Allah (S.A.W) ya kasance yana yin li’itikafi a kowane watan Ramadan kwana goma, amma da shekarar da zai yi wafati ta zo, sai ya yi kwana ashirin. (Bukhari ne ya rawaito).
Falalarsa: Shi li’itikafi ibada ne mai girma wanda yake tsarkake zuciya ga barin shagala da duniya kuma yana sa mutum ya dukufa wajen neman lada da kyakkyawar makoma.
Shigarsa: Ana son shiga li’itikafi kafin faduwar ranar da za a fara.
Ayyukansa: Ana son mai li’itikafi ya shagala da yin ibada kamar nafilfili, karatun Alkur’ani, tasbihi da hailala, zikiri, istigfari, salatin Annabi da sauran ayyukan bin Allah.


SHARADAN INGANCIN I’ITIKAFI
Hakika, li’itikafi yana da sharadan inganci guda bakwai:
1. Musulunci: Li’itikafi ba ya inganta ga kafiri.
2. Balaga: Ba ya inganta ga yaron da bai balaga ba, ko mahaukaci.
3. Tsarki: Ba ya ingantaga mai janaba ko haila ko nifasi.
4. Masallaci: Li’itikafi ba ya inganta a cikin gida ko daki ko Masallacin da ba a sallar jam’i a cikinsa.
5. Azumi: Li’itikafi ba ya inganta ba tare da Azumi ba.
6. Barin runguma ko sunbatar mace da daddare ko da rana.
وَلاَ تُبَاشِرُوهُنَّ وَأَنْتُمْ عَاكِفُونَ فِي الْمَسَاجِدِ. (سورة البقرة: آية 178)
Allah (S.W.T) ya ce: “Kar ku rungume su (mata), lokacin da kuke li’itikafi a cikin Masallaci.” (Suratul Bakara: aya ta 178).
7. Neman iznin miji: Li’itikafin mace ba ya inganta idan mijinta bai yi mata izini ba.


ME KE BATA I’ITIKAFI
Li’itikafi yana baci don aikata babban laifi kamar:
Zina da shan giya da karya da kazafi. Haka nan yana baci don yin jima’i da sumba da daddare ko da rana bisa sha’awa. Haka nan yana baci da zuwan haila, haka nan yana baci da cin abinci ko shan ruwa da rana, haka yana baci in an fita daga Masallaci ba don neman abinci ko wata bukatar dan’adam ba.


DAREN LAILATUL KADARI
Ya zo a cikin Hadisi, ana samun Daren Lailatul Kadari a kwanakin mara na goman karshe na watan Azumi a daren ashirin da daya ko ashirin da uku ko ashirin da biyar ko ashirin da bakwai ko ashirin da tara da dare na karshen watan Ramadan.
Nana Aisha (R.A) ta ce, Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Ku nemi Daren Lailatul Kadari a goman karshe.” (Bukhari ne ya rawaito).
Ana so a yawaita addu’a a Daren Lailatul Kadari. Nana Aisha (R.A) ta ce, na tambayi Manzon Allah (S.A.W)a ce, ya Rasulullahi, idan na ga Daren Lailatul Kadari me zan fada a cikinsa? Sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce, ki ce:
"اللَّهُمَّ إِنَّكَ عَفُوٌّ تُحِبُّ الْعَفْوَ فَاعْفُ عَنِّى."
“Allahumma innaka afuwun tuhibbul afwa fa’afu anni.”
Ma’ana: “Ya Ubangiji, hakika, Kai mai afuwa ne, kuma kana kaunar yin afuwa, ya Allah ka yi min afuwa.” (Bukhari da Muslim ne suka rawaito).
Kuma ana so a karanta wadannan ayoyi masu yawan lada.
1- آيَةُ الْكُرْسِيُّ 2- آمَنَ الرَّسُولُ 3- إِذَا ذُلْزِلَتِ اْلأَرْضُ 4- قُلْ يَأَيُّهَا الْكَافِرُونَ 5- قُلْ هُوَ الله أَحَدٌ 6- سُورَةُ يَاسِين.


1. Ayatal Kursiyyu 2. Amanar-Rasulu 3. Izazul zilatul ardu 4. Kulya ayyuhal kafiruna 5. Kul huwallahu ahad 6. Suratu Yasin.
Kuma a yawaita istigfari, tasbihi, salati ga Annabi, sannan a roki alhairan duniya da na lahira.


SHAIDAR MUTUM DAYA TA WATADAR:- ! ! ! Abdullahi Dan Umar R.A. Ya ruwaito cewa: "An yi duban wata a zamanin Annabi Muhammadu S.A.W. Sai na je na sanar da Annabi S.A.W. Cewa an ga wata, sai ya dau Azumi kuma ya yi umarni da a dauka". ! ! ! ABU DAWUD NE YA RUWAITO SHI. ! ! ! Dan Umar R.A. Ya ce: Manzon Allah S.A.W. Ya ce: "Mu Al'umma ne Ummiyya ba ma rubutu kuma ba ma karatu, shi kwanan wata Ashirin da tara ne ko Talatin". ! ! ! BUKHARI NE YA RUWAITO SHI. ! ! ! Daga Dan Umar R.A. Daga Annabi Muhammadu S.A.W. Ya Ce: "Kada ku yi Azumi har sai kun ga wata kuma kada ku sha har sai kun gan shi. ! ! !Idan kuma aka lullu6e muku sama da gajimare sai kuyi lissafi". ! ! ! ! ! BUKHARI DA MUSLUM NE SUKA RUWAITO SHI. ! ! ! ! Da kuma hadisin dan Abbas R.A. Cewa: "Wani Balarabe ya zo wajen Annabi Muhammadu S.A.W. Sai ya ce: "Lallai na ga watan Azumi (Ramadan)". ! ! Sai Annabi Muhammadu S.A.W. Ya tambaye shi cewa: "Ka shaida cewa ba wani abin bautawa da gaskiya sai Allah?" ! ! ! Sai ya ce: "Kwarai". ! ! Sannan sai Annabi Muhammadu S.A.W. Ya sake tambayarsa ya ce: "Ka shaida cewa Muhammadu S.A.W. Manzon Allah Ne?" ! ! ! Sai ya ce: "Kwarai kuwa". ! ! ! Sai Ya ce: Bilal a yi sanarwa cewa mutane su fara Azumi". ! ! ! ! AHMAD NE YA RUWAITO SHI. ! ! ! ! ! ! ! ! ! ! !


GANIN MUTUM DAYA:- ! ! ! ! ! Duk Mutumin da ya ga watan Azumi (Ramadan) shi kadai sai ya yi Azumi, saboda fadin Allah Ta'ala: "Duk wanda ya halarci watan Azumi (Ramadan) sai ya yi Azumi". ! ! Suratul Bakarati Aya Ta 185. ! ! ! Haka Kuma Da Hadisin Annabi Muhammadu S.A.W. Wanda ya ce: "Ku yi Azumi da zarar an ga wata, kuma ku sha da zarar an ga wata". ! ! Sai dai abin da aka fi so shi ne idan mutum shi kadai ya ga wata kuma ya dau Azumi to sai ya yi a 6oye, tun da shi Azumin ya kamashi". ! ! ! ! ! ! ! ! ! ! ! !


BANBANCIN KASA, Kowacce Kasa Ya Halatta Su (Fara) Yin Azumin Su Daban. ! ! ! ! ! Saboda hadisin Kuraibu bawan Abdullahi Dan Abbas R.A. Ya ce: "Na baro kasar Sham alhali watan Ramadan ya kama a lokacin da nake can. Mun ga watan ne a ranar juma'a. Daga nan sai na zo birnin Madina a karshen wata. Sai Dan Abbas R.A. Ya tambaye Ni cewa: "Yaushe kuka ga wata?" Sai na ce: "A ranar Juma'a". Sai ya ce da Ni: "Kai ma a ranar Juma'a ka ga watan?" Sai na ce: "Kwarai kuwa, kuma mutane sun yi Azumi tare da Mu'awiyya". Sai ya ce: "Amma mu kuwa ranar Asabar muka gan shi, kuma za mu ci gaba da yin Azumi har sai mun kai kwana Talatin ko kuma mun ga wata". Sai na ce da Shi: "Shin ba za ku yi amfani da ganin Mu'awiyya ba?" Sai ya ce: "A'a, domin haka Manzon Allah S.A.W. Ya umarce mu da mu aikata". Muslim Da Abu Dawud Ne Suka Ruwaito Shi. ! ! ! ! ! Daga Dan Mas'ud R.A. Ya ce: "Mun yi Azumi Ashirin da tara tare da Annabi Muhammadu S.A.W. Fiye da yadda muka yi Azumi Talatin". (Wato wasu watannin ba sa cika). Abu Dawuda Da Tirmizi Ne Suka Ruwaito Shi. ! ! ! ! ! Daga Sa'adu Dan Amru R.A. Al~Amawi ya ce: "An ce wa Nana A'isha R.A. An ga wannan watan ne fa da kwana ashirin da tara". Sai ta ce; "Mamakin mai kuke yi game da ganin wata Ashirin da tara? Na ranste da Allah, Azumin da muka yi tare da Manzon Allah S.A.W. Kwana Ashirin da tara ya fi Azumin da muka yi kwana Talakatin yawa". (Malam Haisami ya ce: "Ahmadu ne ya ruwaito shi da Dabarani, kuma wadanda suka ruwaito wannan hadisi, a ruwayar Ahmad masu ruwaya ne a Sahihul Bukhari). ! ! ! ! ! Daga Dan Umar R.A. Hakika Annabi S.A.W. Ya ce "wata kwana Ashirin da tara ne, kada ku yi Azumi sai kun ga wata, idan sama ta yi gajimare, ku cika kwana talatin". Bukhari Ne Ya Ruwaito Shi. ! ! ! ! ! A ruwayar Muslim ce wa ya yi Annabi Muhammadu S.A.W. Ya ambaci Ramadan, sai ya hada hannayensa ya ce: "Wata haka ne da haka da haka". (Sannan Ya Makale Babbban Dan Yatsa A Karo Na Uku) Ya ce: "Ku yi azumi da ganin wata, kuma ku sha da ganin wata (Watan Sallah). Idan gargije ya yi yawa a sama to ku cika kwana Talatin". (Wato Idan Ba Ku Ga Wata Ba). ! ! ! Imam Shafi'I Da Imam Baihaki Da Darul Kudni sun fitar daga Fatima 'Yar Hussaini, hakika wani mutum ya bayar da shaida cewa yaga watan Azumi a gaban Sayyidina Aliyi R.A./A.S. Sai Sayyidina Aliyu R.A./A.S. Ya yi Azumi ya kuma Umarci mutane su yi Azumi, sannan ya ce: "Na rantse da Allah a ce na yi Azumi a watan Sha'aban ya fi soyuwa a gare Ni, da in sha a cikin Azumin watan Ramadan". ! ! ! ! ! ! ! ! ! ! ! !


YIN AZUMI TARE KO DABAN~DABAN WANNE YA FI DACEWA ??? ! ! ! ! ! Abin da ya fi dacewa da koyarwar Annabi Muhammadu S.A.W. Shi ne Musulmai su yi Azumi a lokaci daya. Idan kuma ba haka bai samu ba, to sai kowanne gari su yi Azumi a lokaci daya, koda kuwa su kasashen suna karkashin Sarki daya ko Sarakuna Daban~Daban. ! ! Amma dai ba shi yiwuwa dayansu ya ke6anta ko wata kungiyar Jama'a da yin Azumi ko bikin Sallah ko da kuwa ya ga watan Azumi shi kadai. Wannan shi ne hukunci mafi rijaye saboda fadin Manzon Allah S.A.W. "Kuma Sallarku ita ce ranar da duk gari suke yin layya". Da kuma fadinsa S.A.W. "Azumi shi ne ranar da kuke yin Azumi (Gaba Daya) kuma Sallah ita ce ranar da kuke yi gaba daya. Haka nan Layya ita ce ranar da kuke yi gaba daya". Tirmizi Da Abu Dawuda Ne Suka Ruwaito Shi. ! ! ! Ya kamata ga mutanen da suke zaune a kasar da ba Musulmai ne suke da rinjaye ba, ko kuma wajen da Musulmai suke da rinjaye, su rika yi biyayya ga hukumar da take sanar da ganin wata ba tare da sun rarraba kai ba. Idan kuma ba su da hukuma sai su yi koyi da garin da ya fi kusa da su, kuma da daukar Azumi tare. Kuma an fi so su yi ko yi da garin da yake yamma da su, domin ya zamanto watan ya fara fitowa a wasu wurare". ! ! ! ! ! Zai iya yiwuwa Azumi ya kai tsawon awa goma sha daya ko fiye a wasu garuruwa ko kuma ya kasance awa biyar. Sai dai abin da ya fi wajaba a kansu shi ne abin da Allah Ya fada cewa: "Ku ci ku sha har sai farin zare ya bayyana a gare ku daga bakin zare na Alfijir, sannan ku cika Azumi zuwa dare". ! ! ! Su kuma garuruwan da rana ba ta faduwa a lokacin zafi kuma ba ta hudowa a lokacin sanyi sai su kwantanta lokacin. Wato mutanen sai su yi la'akari da garin da yake kusa da su a wajen tantance dare da rana. Haka ma za su yi a lokacin Sallah da Azumi da sauran Ibadu, saboda fadin Annabi Muhammadu S.A.W. Game da zuwan Dujal zai bayyana tsawon kwana arba'in. Kwana arba'in kamar shekara, kwana daya kamar wata, kuma kwana daya kamar sati daya, sauran kwanakinsa kuwa kamar kwanakinku suke". Sai muka ce: "Ya Manzon Allah S.A.W. Wannan kwana kamar shekara, Sallar kwana daya za ta ishe Mu? Sai ya ce: "A'a" sai dai ku rika kwatanta lokuta". Muslim Ne Ya Ruwaito Shi. ! ! ! ! ! ! ! ! ! ! ! ! ! ! ! ! !




FADAKARWA ! ! ! ! Ya wajaba Musulmai su hada kai waje guda game da ganin wata da Sallar Idi, kuma yana da kyau lallai Musulami su hada kai wajen ganin kowanne wata ba sai na Azumi (Ramadan) ba, kusan a yanzu babu wani wata da Musulmai suka fi damuwa da shi irin watan Azumu (Ramadan) ba sa jayayya da ranar Arfat, da ranar Idin Babbar Sallah kamar yadda suke jayayya da daukar Azumi ko sauke shi. ! ! ! Kuma Jahilai sun shiga cikin lamarin ganin wata da karfi, idan Azumin ya huce babu ruwansu da kowanne wata, kuma babu wani wata wanda ake jayayya a kansa sai na Azumi (Ramadan) ! ! Wadansu suna yi ne iya fahimtarsu ! ! ! Wadansu suna yi don Jahilci ! ! ! Wadansu kuma wane ya ce: saboda haka na yarda da duk abin da ya ce;, ! ! Wadansu kuma in ba Malaminsu ne ya ce su dauka ko su sauke ba, ba za su yi ba, to akwai babban hatsari, ganin wannan ya sa na dan tattaro kadan daga Hadisan Annabi Muhammadu S.A.W. Da fahimtar da Malamai suka yi wa Hadisan, kuma suka fassara su don samun masalaha ga Al'ummar Musulmai game da daukar Azumi kosauke shi. ! ! ! Mai alfarma Sarkin Musulmai shi ne yake sanar da labarin ganin wata ta hanyar Sarakuna na Musulunci wadanda suke tare da shi, su kuma Sarakuna, suna sanya Malaman Addinin Musulunci a gaba, da Limamai, su ne suke tambayoyi ga dukkan wanda ya ce yaga wata, su tambaye shi saboda Allah, yaya ya ga watan a dai-dai ina? ! ! Dama yake kallo, ko hagu, ko sama yake kallo, a dai-dai wacce kusurwa ya ke, yamma ko dama ko hagu, idan sun gamsu, sai su gaya/fada wa Martaba Sarakuna ko mai alfarma Sarkin Musulmi, daga nan sai ya sanarwa ganin wata, shi ganin wata Amana ce tsakaninmu da Shuwagabanninmu, ba Radiyo ba ce ko Talabijin suke fadar ganin wata, a'a dan uwanka ne yake shiga ciki ya fada wanda ka bawa amana, saboda haka nake jawo hankalin mutane, mu karanta wadannan hadisai karatun nutsuwa da tunani mai kyau da kyakykyawar zuciya, don mu huta ga barin yin jayyaya kowacce shekara. ! ! ! ! In har kana da Malami shi ma yana da Malami, yana yiwuwa fahimtar wani Malamin da karatu, ya fi fahimtar Malaminka. ! ! ! ! Babu shakka mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar Na 3 yana iya bakin kokarinsa game da hada kan Musulmai na Najeriya kamar yadda Marigaji Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Dr. Ado Bayaro Ya Dinga Yin Kokarin ganin kawunan Musulmai ya hadu waje daya ta fuskar daukar Azumi da sauke shi da yin sallar Idi tare, da kuma ganin hadin kan Musulmai makwabta da duniya baki daya, game da hakkin da ya rataya a wuyansu, ! ! Haka Shima Mai martaba na yanzu Alhaji Sanusi Lamido Sanusi Na 2 yake kokarin dorawa daga inda ya gada. Allah Ka Kara karfafarsu, ameeeeen. ! ! ! Ya kamata kowanne Musulmi ya yi kyakykyawar addu'a, ga mai martaba Sarkin Musulmi da sauran Sarakun Musulunci baki daya, allah Ya kara musu Lafiya, ya ba su ikon hada kan musulmai, tare da shugabancin Najeriya, baki daya ameeeeeen ! ! ! ! Allah Ka kara haskaka kabarin Marigaji Mai martaba, Alhaji Dr. Ado Bayero, ammeeeeeeen


Allah Madaukain Sarki Ya Ce: "Ya ku wadanda kuka ba da gaskiya, an wajabta Azumi a kanku kamar yadda aka wajabta shi a kan wadanda suka gabace ku, (An Yi Haka Ne) Don ku yi tsoron Allah. 'Yan kwanaki ne kidayayyu; wanda kuwa yana cikin tafiya, (Ya Sha Azumi) sai ya cika adadin abin da ya sha daga wasu kwanaki. ! ! ! ! ! Kuma fansa ta ciyar da Miskini tana kan wanda suka sha tare da ikon yin sa (Da Kyar). ! ! ! Wanda Ya kara (Ita Fansar) don samun lada wannan shi fi masa Alkhairi. ! ! ! ! ! Amma kuma ku yi Azumin (Shi Ya Fi) Alkhairi a gare ku idan kun kasance kun san (Haka, To Sai Ku Aikata Shi). (Wannan Shi Ne) watan Azumi wanda aka saukar da Alqur'ani a cikinsa, don shiriya ga mutane da (Ayoyi) Mabayyana na shiriya da rarrabewa tsakanin karya da gaskiya. ! ! ! ! ! (Wanda Ya Rayu Cikinku Har Zuwa Watan Ko Sai Ya Azumce Shi, Kuma Wanda Ya Kasance Marar Lafiya Ko A Cikin Tafiya Sai Ya Yi Adadin Wasu Kwanakin (Dai-dai Yawan Wadanda Ya Sha). ! ! ! ! ! Allah Yana nufin sauki ne a gare ku, kuma ba Yana nufin wahalar da ku ba ne, don ku cika adadin kwanakin don kuma ku girmama Allah A bisa abin da Ya Shirye ku, ko kwa gode wa (Ni'imominsa). ! ! ! ! ! Idan bayina suka tambaye ka game da Ni tYa Muhammadu S.A.W. Ka Ce Da Su): Hakika Ni a kusa nake, ina amsa addu'ar mai addu'a idan ya roke Ni; saboda haka su nemi biyan bukata gare Ni, kuma su ba da gaskiya da Ni don su shiriya. ! ! ! ! ! An halatta muku tarawa da matayen ku a daren Azumi; Su sutura ne a gare ku, ku kuma sutura ne a gare su. Ubangiji ya san cewa hakika kun kasance kuna ha'intar kanku, sai Ya kar6i tubanku kuma Ya yafe muku (Ba Tare Da Ya Yi Muku Azaba Ba); To yanzu ku rungume su, ku nemi abin da Allah Ya halatta muku, kuma ku ci ku sha har sai farin kwalle ya bayyana a gare ku daga bakin kwalle na Alfijir (Watau Har Izuwa Fitowar Alfijiri); sannan ku cika Azumi zuwa dare. Kada ku rungume su idan kuna lazimtar idaba cikin Masallatai. Wadancan iyakokin Allah Ne, to kada ku kusance su. Kamar haka Alllah Yake bayyana ayoyinsa ga mutane don su tsorata". ! ! ! ! ! Allah Ta'ala Ya ce: "Hakika. Mu Muka saukar da shi a cikin dare mai albarka. Hakika Mu Mun kasancce masu garkadi". ! Suratul Duhani Aya Ta 2. ! ! ! ! ! Allah Ta'ala Ya Ce: "Da masu Azumi maza da mata, da masu kiyaye tsiraicinsu maza,da mata masu kiyaye tsiraicinsu, da maza masu ambaton Allah da Yawa, da Mata masu ambaton Allah da yawa, dukkaninsu Allah Ya yi musu tanadin Gafara da Lada mai girma". ! Suratul Ahzab Aya Ta 35-36. ! ! ! ! ! Allah Ta'la Ya Ce: "Ku ci ku sha, kuna masu farin ciki, saboda abin da kuka gabatar a kwanakinku da suka wuce (Na Duniya) ! ! Suratul Hakati Aya Ta 24.


YAYA AZUMI YAKE WAJABA? ! ! ! ! ! Azumin Ramadan yana wajaba da zarar an ga wata ko idan watan Sha'aban ya cika kwana talatin a kan haka Azumi yana wajaba da zarar dayan abu biyu ya tabbata a saboda Hadisin Dan Umar R.A. Ya ce: Manzon Allah S.A.W. Ya Ce: "Ku yi Azumi da zarar kun ga wata, kuma ku sha ruwa da zarar kun ga wata. ! ! Idan gajimare ya lullu6e sama, sai a cika kwanakin Sha'aban Talatin". ! ! ! ! ! BUKHARI DA MUSLIM NE SUKA RUWAITO SHI.


SHAIDAR MUTUM DAYA TA WATADAR:- ! ! ! Abdullahi Dan Umar R.A. Ya ruwaito cewa: "An yi duban wata a zamanin Annabi Muhammadu S.A.W. Sai na je na sanar da Annabi S.A.W. Cewa an ga wata, sai ya dau Azumi kuma ya yi umarni da a dauka". ! ! ! ABU DAWUD NE YA RUWAITO SHI. ! ! ! Dan Umar R.A. Ya ce: Manzon Allah S.A.W. Ya ce: "Mu Al'umma ne Ummiyya ba ma rubutu kuma ba ma karatu, shi kwanan wata Ashirin da tara ne ko Talatin". ! ! ! BUKHARI NE YA RUWAITO SHI. ! ! ! Daga Dan Umar R.A. Daga Annabi Muhammadu S.A.W. Ya Ce: "Kada ku yi Azumi har sai kun ga wata kuma kada ku sha har sai kun gan shi. ! ! !Idan kuma aka lullu6e muku sama da gajimare sai kuyi lissafi". ! ! ! ! ! BUKHARI DA MUSLUM NE SUKA RUWAITO SHI. ! ! ! ! Da kuma hadisin dan Abbas R.A. Cewa: "Wani Balarabe ya zo wajen Annabi Muhammadu S.A.W. Sai ya ce: "Lallai na ga watan Azumi (Ramadan)". ! ! Sai Annabi Muhammadu S.A.W. Ya tambaye shi cewa: "Ka shaida cewa ba wani abin bautawa da gaskiya sai Allah?" ! ! ! Sai ya ce: "Kwarai". ! ! Sannan sai Annabi Muhammadu S.A.W. Ya sake tambayarsa ya ce: "Ka shaida cewa Muhammadu S.A.W. Manzon Allah Ne?" ! ! ! Sai ya ce: "Kwarai kuwa". ! ! ! Sai Ya ce: Bilal a yi sanarwa cewa mutane su fara Azumi". ! ! ! ! AHMAD NE YA RUWAITO SHI.


GANIN MUTUM DAYA:- ! ! ! ! ! Duk Mutumin da ya ga watan Azumi (Ramadan) shi kadai sai ya yi Azumi, saboda fadin Allah Ta'ala: "Duk wanda ya halarci watan Azumi (Ramadan) sai ya yi Azumi". ! ! Suratul Bakarati Aya Ta 185. ! ! ! Haka Kuma Da Hadisin Annabi Muhammadu S.A.W. Wanda ya ce: "Ku yi Azumi da zarar an ga wata, kuma ku sha da zarar an ga wata". ! ! Sai dai abin da aka fi so shi ne idan mutum shi kadai ya ga wata kuma ya dau Azumi to sai ya yi a 6oye, tun da shi Azumin ya kamashi".


BANBANCIN KASA, Kowacce Kasa Ya Halatta Su (Fara) Yin Azumin Su Daban. ! ! ! ! ! Saboda hadisin Kuraibu bawan Abdullahi Dan Abbas R.A. Ya ce: "Na baro kasar Sham alhali watan Ramadan ya kama a lokacin da nake can. Mun ga watan ne a ranar juma'a. Daga nan sai na zo birnin Madina a karshen wata. Sai Dan Abbas R.A. Ya tambaye Ni cewa: "Yaushe kuka ga wata?" Sai na ce: "A ranar Juma'a". Sai ya ce da Ni: "Kai ma a ranar Juma'a ka ga watan?" Sai na ce: "Kwarai kuwa, kuma mutane sun yi Azumi tare da Mu'awiyya". Sai ya ce: "Amma mu kuwa ranar Asabar muka gan shi, kuma za mu ci gaba da yin Azumi har sai mun kai kwana Talatin ko kuma mun ga wata". Sai na ce da Shi: "Shin ba za ku yi amfani da ganin Mu'awiyya ba?" Sai ya ce: "A'a, domin haka Manzon Allah S.A.W. Ya umarce mu da mu aikata". Muslim Da Abu Dawud Ne Suka Ruwaito Shi. ! ! ! ! ! Daga Dan Mas'ud R.A. Ya ce: "Mun yi Azumi Ashirin da tara tare da Annabi Muhammadu S.A.W. Fiye da yadda muka yi Azumi Talatin". (Wato wasu watannin ba sa cika). Abu Dawuda Da Tirmizi Ne Suka Ruwaito Shi. ! ! ! ! ! Daga Sa'adu Dan Amru R.A. Al~Amawi ya ce: "An ce wa Nana A'isha R.A. An ga wannan watan ne fa da kwana ashirin da tara". Sai ta ce; "Mamakin mai kuke yi game da ganin wata Ashirin da tara? Na ranste da Allah, Azumin da muka yi tare da Manzon Allah S.A.W. Kwana Ashirin da tara ya fi Azumin da muka yi kwana Talakatin yawa". (Malam Haisami ya ce: "Ahmadu ne ya ruwaito shi da Dabarani, kuma wadanda suka ruwaito wannan hadisi, a ruwayar Ahmad masu ruwaya ne a Sahihul Bukhari). ! ! ! ! ! Daga Dan Umar R.A. Hakika Annabi S.A.W. Ya ce "wata kwana Ashirin da tara ne, kada ku yi Azumi sai kun ga wata, idan sama ta yi gajimare, ku cika kwana talatin". Bukhari Ne Ya Ruwaito Shi. ! ! ! ! ! A ruwayar Muslim ce wa ya yi Annabi Muhammadu S.A.W. Ya ambaci Ramadan, sai ya hada hannayensa ya ce: "Wata haka ne da haka da haka". (Sannan Ya Makale Babbban Dan Yatsa A Karo Na Uku) Ya ce: "Ku yi azumi da ganin wata, kuma ku sha da ganin wata (Watan Sallah). Idan gargije ya yi yawa a sama to ku cika kwana Talatin". (Wato Idan Ba Ku Ga Wata Ba). ! ! ! Imam Shafi'I Da Imam Baihaki Da Darul Kudni sun fitar daga Fatima 'Yar Hussaini, hakika wani mutum ya bayar da shaida cewa yaga watan Azumi a gaban Sayyidina Aliyi R.A./A.S. Sai Sayyidina Aliyu R.A./A.S. Ya yi Azumi ya kuma Umarci mutane su yi Azumi, sannan ya ce: "Na rantse da Allah a ce na yi Azumi a watan Sha'aban ya fi soyuwa a gare Ni, da in sha a cikin Azumin watan Ramadan".

YIN AZUMI TARE KO DABAN~DABAN WANNE YA FI DACEWA ??? ! ! ! ! ! Abin da ya fi dacewa da koyarwar Annabi Muhammadu S.A.W. Shi ne Musulmai su yi Azumi a lokaci daya. Idan kuma ba haka bai samu ba, to sai kowanne gari su yi Azumi a lokaci daya, koda kuwa su kasashen suna karkashin Sarki daya ko Sarakuna Daban~Daban. ! ! Amma dai ba shi yiwuwa dayansu ya ke6anta ko wata kungiyar Jama'a da yin Azumi ko bikin Sallah ko da kuwa ya ga watan Azumi shi kadai. Wannan shi ne hukunci mafi rijaye saboda fadin Manzon Allah S.A.W. "Kuma Sallarku ita ce ranar da duk gari suke yin layya". Da kuma fadinsa S.A.W. "Azumi shi ne ranar da kuke yin Azumi (Gaba Daya) kuma Sallah ita ce ranar da kuke yi gaba daya. Haka nan Layya ita ce ranar da kuke yi gaba daya". Tirmizi Da Abu Dawuda Ne Suka Ruwaito Shi. ! ! ! Ya kamata ga mutanen da suke zaune a kasar da ba Musulmai ne suke da rinjaye ba, ko kuma wajen da Musulmai suke da rinjaye, su rika yi biyayya ga hukumar da take sanar da ganin wata ba tare da sun rarraba kai ba. Idan kuma ba su da hukuma sai su yi koyi da garin da ya fi kusa da su, kuma da daukar Azumi tare. Kuma an fi so su yi ko yi da garin da yake yamma da su, domin ya zamanto watan ya fara fitowa a wasu wurare". ! ! ! ! ! Zai iya yiwuwa Azumi ya kai tsawon awa goma sha daya ko fiye a wasu garuruwa ko kuma ya kasance awa biyar. Sai dai abin da ya fi wajaba a kansu shi ne abin da Allah Ya fada cewa: "Ku ci ku sha har sai farin zare ya bayyana a gare ku daga bakin zare na Alfijir, sannan ku cika Azumi zuwa dare". ! ! ! Su kuma garuruwan da rana ba ta faduwa a lokacin zafi kuma ba ta hudowa a lokacin sanyi sai su kwantanta lokacin. Wato mutanen sai su yi la'akari da garin da yake kusa da su a wajen tantance dare da rana. Haka ma za su yi a lokacin Sallah da Azumi da sauran Ibadu, saboda fadin Annabi Muhammadu S.A.W. Game da zuwan Dujal zai bayyana tsawon kwana arba'in. Kwana arba'in kamar shekara, kwana daya kamar wata, kuma kwana daya kamar sati daya, sauran kwanakinsa kuwa kamar kwanakinku suke". Sai muka ce: "Ya Manzon Allah S.A.W. Wannan kwana kamar shekara, Sallar kwana daya za ta ishe Mu? Sai ya ce: "A'a" sai dai ku rika kwatanta lokuta". Muslim Ne Ya Ruwaito Shi.


SUNNONIN AZUMI SHIDA NE:- ! ! ! 1. Jinkirta yin Sahur zuwa karshen dare ga wanda ba ya tsoron fitowar Alfijir. ! ! ! 2. Gaggauta buda baki idan an tabbatar da faduwar rana ! ! ! 3. Yawaita ayyukan alkhairi musamman kiyaye Salloli biyar a cikin Jam'I da bayar da Zakka ga wanda ya cancanta, da kuma yawaita nafiloli da sadaka da karatun Alqur'ani da sauran ayyukan Alkhairi ! ! ! 4. Haka nan idan an zage shi ya ce: "Ni Azumi nake yi ba tare da ya rama zagin ba ko ya munana wa wanda ya munana masa sai dai ya kyautata masa domin ya samu lada kuma ya ku6uta daga Zunubai" ! ! ! 5. Kuma ya yi Addu'a a lokacin buda baki da abin da ya ga dama. A cikin Addu'o'in akwai "Ya Ubangiji Don Kai Na Yi Azumi, Kuma Da arzikinKa Na Yi Buda Baki, Ya Ubangiji Ka Kar6i Wannan Azumi Nawa, Lallai Kai Mai Ji Ne, Kuma Masani" ! ! ! 6. Kuma ya yi buda baki da danyen abu, ko dabino ko ruwa. ! ! ! ! ! ! ! ! ! ! ! ! ! ! ! ! !

SUNNONIN AZUMI SHIDA NE:- ! ! ! 1. Jinkirta yin Sahur zuwa karshen dare ga wanda ba ya tsoron fitowar Alfijir. ! ! ! 2. Gaggauta buda baki idan an tabbatar da faduwar rana ! ! ! 3. Yawaita ayyukan alkhairi musamman kiyaye Salloli biyar a cikin Jam'I da bayar da Zakka ga wanda ya cancanta, da kuma yawaita nafiloli da sadaka da karatun Alqur'ani da sauran ayyukan Alkhairi ! ! ! 4. Haka nan idan an zage shi ya ce: "Ni Azumi nake yi ba tare da ya rama zagin ba ko ya munana wa wanda ya munana masa sai dai ya kyautata masa domin ya samu lada kuma ya ku6uta daga Zunubai" ! ! ! 5. Kuma ya yi Addu'a a lokacin buda baki da abin da ya ga dama. A cikin Addu'o'in akwai "Ya Ubangiji Don Kai Na Yi Azumi, Kuma Da arzikinKa Na Yi Buda Baki, Ya Ubangiji Ka Kar6i Wannan Azumi Nawa, Lallai Kai Mai Ji Ne, Kuma Masani" ! ! ! 6. Kuma ya yi buda baki da danyen abu, ko dabino ko ruwa. ! ! ! ! ! ! ! ! ! ! ! ! ! ! ! ! !

"Nawaitu An Asuma Fardas~Saumur~R amadan, Thalathunaaw Tis'a Wa'ishiruna Yauma Lillahi Ta'ala". ! ! ! ! ! Nawaitu Farda Saumur~Ramadan Lillahi Ta'ala".
! !! ! ! ! ! ! ! ! ! ! !


Abu Sa'I'd Alkhudri R.A. Ya ruwaito ya ce: Manzon Allah S.A.W. Ya ce: "Lallai watan Ramadan watan Al'ummata ne, shi ya sa idan dayansu ya yi rashin lafiya sai su je duba shi, kuma idan dayansu yana Azumi ba ya karya ko cin naman wani kuma yana mai buda baki cikin nutsuwa yana mai kare Farillar da Allah Ya dora masa. A karshe kuma zai fita daga zunubansa kamar yadda macijiya take yin sa6a". ABUSSHAIKH NE YA RUWAITO SHI. ! ! ! ! !


Abu Sa'I'd Alkhudri R.A. Ya ruwaito ya ce: Manzon Allah S.A.W. Ya ce: "Lallai watan Ramadan watan Al'ummata ne, shi ya sa idan dayansu ya yi rashin lafiya sai su je duba shi, kuma idan dayansu yana Azumi ba ya karya ko cin naman wani kuma yana mai buda baki cikin nutsuwa yana mai kare Farillar da Allah Ya dora masa. A karshe kuma zai fita daga zunubansa kamar yadda macijiya take yin sa6a". ABUSSHAIKH NE YA RUWAITO SHI. 


GABATARWA:- ! ! ! ! ! Godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki, wanda Ya saukar da Alqur'ani cikin Watan Ramadan daren Lailatul Kadari Ya sanya Azumi garkuwa ga barin shiga Wuta, Rahama ga Muminai, tsira da aminci su tabbata ga Annabi Muhammadu S.A.W. Wanda ya ce: "Wanda Ya tsaya daren Lailatul Kadri yana mai Imani da neman yardar allah, to Allah Ya gafarta masa abin da ya gabata daga laifukansa". ! ! ! ! Ina mai farin cikin gabatarwa da 'yan uwana wasu rubuce-rubuce akan fa'idan da yake tattare a cikin watan Ramadan wanda ya kunshi kadan daga Falalar watan Ramadan mai albarka, don ya zamo wani Babban haske game da Azumi a wajen 'yan uwana Almajirai. ! ! Karanta Hadisai masu albarka ga Musulmai Mumini, zai kara masa ganin girman Azumi, da kwadayin neman yardar Allah A cikin Watan. ! ! ! Ina Mai kara godiya ga Allah S.W.T. Da ya bani ikon tattaro Hadisai, Na Manzon Allah S.A.W. Wanda suka yi Magana game da Azumin Watan Ramada, Allah Ka yi sakayya da gidan Aljanna, Ga Malamai Magabata wadanda suka rubuta Alkhairi suka bar mana, wanda a cikin Littattafansu na samo wadannan hadisai, na tattara su, na fassarasu da taimakon bayin Allah, don Amfanin 'Yan uwa musulmai (Irin Mu Almajirai) ! ! Kamar Imamul Bukhari, Imamul Muslim, Imamul Baihaki, Imamul Dan Majah, Imamul Tirmizi, Imamun Nasa'I, Imam Dan Hibban, Imamu Dan Huzaimata, Imam Malik, Imamul Bazzar, Imamu Dabarani, Imamu Suyudi, Imamu Asbihani, Imamu Ahmad, Imamu Abu Dawuda, Imamu Hafiz Abu Muhammad Zakiyyudden Abdul'azim Bin Abdul Kawiyyi Al~Munzari. ! ! ! ! Allah Ya kijansu, da Sauran Bayin Allah, Allah Ya saka musu da Alkhairi, AmeeeN. ! ! ! ! Ina kira ga sauran 'yan uwana Almajirai mu kasance da juna cikin wannan wata mai albarka da amfanuwa da juna akan ayoyi da hadisai da zamu fadakarwa da junanmu dan amfanuwa. ! ! ! ! Ya kamata kowanne Musulmi Namiji da Mace, ya fahimci koda kadan daga Wadannan Hadisai masu albarka da zasu dinga zuwa insha Allahu a cikin watan Ramadan don sanin matsayin Azumin watan Ramadan, Allah Dan Sirrin Manzon Allah S.A.W. Kayi mana Gam Da Katar. ! ! ! ! AmeeeeeN SummA AmeeeeeN !!!


GODIYA:- ! ! ! ! Godiya ta tabbata ga Allah Mai girma da daukaka, Mahaliccin talikai, Mai shiryar da wanda ya so, Mai Azurta wanda ya so, mai kaskantar da wanda ya so, mai daga Daraja ga wanda ya so, mai kar6ar Ayyuka na Alkhairi ga wanda ya so, tsira da aminci su kara tabba ga Annabi Muhammadu S.A.W. Dan Abdullahi cikamakin Annabawa da Manzanni, wanda ya kar6o sako daga Allah, Ya sanar da Al'ummarsa mai albarka, din ya fitar da su daga duhun kafirci zuwa hasken Imani. ! ! ! ! Allah Ya kara tsira da aminci a gare Shi, kamar yadda ya zo mana da Alqur'ani mai girma, a cikinsa ne muka ga Albarkar Azumin watan ramadan, tare da wajabcinsa ga Muminai masu iko, kuma saukar da shi a daren "LAILATUL KADRI. ! ! ! ! Babu shakka ba karamar Rahama Allah Madaukaki Ya ba mu ba, a cikin watan Azumi (Daure 6atattun Shaidanu) don kada su 6ata Azumin masu azumi, ga yawan gafara da yafewa, da kar6ar addu'o'I, da bude kofofin Rahama, da kulle kofofin Azaba ga masu Azumi. ! ! ! ! Ya wajaba ga kowanne musulmi mai hankali ya kiyaye alfarmar wannan watan da yawaita yin Alkhairi a cikinsa, kamar ba da abinci, kamar shayar da ruwa, kamar yawaita karatun Alqur'ani Ya waita "Istigfari" da yawaita yin Salati ga Annabi Muhammadu S.A.W. Da kame baki da jiki da barin munanan abubuwa. ! ! ! ! Allah Ya kar6i Azuminmu, Allah Ya kar6i tsayiwar darenmu, Allah Ya kar6i sauran Ibadinmu, Allah Ya sa mu cikin wadanda yake yi wa gafara, allah Ya jikan Iyayenmu, Allah Ya Shirya Zuri'armu, Allah Ya sa bayanmu ta yi kyaun alla Ka azurta mu cikawa da Imani, Allah Ya sa mu samu kabarinmu dausayi ne daga dausayin Aljanna, Allah Ka rufa mana asiri duniya da lahira, Malamanmu na Addinin Musulunci Allah Ya saka musu da Alkhairi, Allah Ya kara tsira da Aminci ga Annabi Muhammadu S.A.W. Da Alayensa da Sahabbansa da Matayensa masu tsarki, da sauran Masoyansa har zuwa ranar karshe. ! ! !


FADAKARWA ! ! ! ! Ya wajaba Musulmai su hada kai waje guda game da ganin wata da Sallar Idi, kuma yana da kyau lallai Musulami su hada kai wajen ganin kowanne wata ba sai na Azumi (Ramadan) ba, kusan a yanzu babu wani wata da Musulmai suka fi damuwa da shi irin watan Azumu (Ramadan) ba sa jayayya da ranar Arfat, da ranar Idin Babbar Sallah kamar yadda suke jayayya da daukar Azumi ko sauke shi. ! ! ! Kuma Jahilai sun shiga cikin lamarin ganin wata da karfi, idan Azumin ya huce babu ruwansu da kowanne wata, kuma babu wani wata wanda ake jayayya a kansa sai na Azumi (Ramadan) ! ! Wadansu suna yi ne iya fahimtarsu ! ! ! Wadansu suna yi don Jahilci ! ! ! Wadansu kuma wane ya ce: saboda haka na yarda da duk abin da ya ce;, ! ! Wadansu kuma in ba Malaminsu ne ya ce su dauka ko su sauke ba, ba za su yi ba, to akwai babban hatsari, ganin wannan ya sa na dan tattaro kadan daga Hadisan Annabi Muhammadu S.A.W. Da fahimtar da Malamai suka yi wa Hadisan, kuma suka fassara su don samun masalaha ga Al'ummar Musulmai game da daukar Azumi kosauke shi. ! ! ! Mai alfarma Sarkin Musulmai shi ne yake sanar da labarin ganin wata ta hanyar Sarakuna na Musulunci wadanda suke tare da shi, su kuma Sarakuna, suna sanya Malaman Addinin Musulunci a gaba, da Limamai, su ne suke tambayoyi ga dukkan wanda ya ce yaga wata, su tambaye shi saboda Allah, yaya ya ga watan a dai-dai ina? ! ! Dama yake kallo, ko hagu, ko sama yake kallo, a dai-dai wacce kusurwa ya ke, yamma ko dama ko hagu, idan sun gamsu, sai su gaya/fada wa Martaba Sarakuna ko mai alfarma Sarkin Musulmi, daga nan sai ya sanarwa ganin wata, shi ganin wata Amana ce tsakaninmu da Shuwagabanninmu, ba Radiyo ba ce ko Talabijin suke fadar ganin wata, a'a dan uwanka ne yake shiga ciki ya fada wanda ka bawa amana, saboda haka nake jawo hankalin mutane, mu karanta wadannan hadisai karatun nutsuwa da tunani mai kyau da kyakykyawar zuciya, don mu huta ga barin yin jayyaya kowacce shekara. ! ! ! ! In har kana da Malami shi ma yana da Malami, yana yiwuwa fahimtar wani Malamin da karatu, ya fi fahimtar Malaminka. ! ! ! ! Babu shakka mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar Na 3 yana iya bakin kokarinsa game da hada kan Musulmai na Najeriya kamar yadda Marigaji Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Dr. Ado Bayaro Ya Dinga Yin Kokarin ganin kawunan Musulmai ya hadu waje daya ta fuskar daukar Azumi da sauke shi da yin sallar Idi tare, da kuma ganin hadin kan Musulmai makwabta da duniya baki daya, game da hakkin da ya rataya a wuyansu, ! ! Haka Shima Mai martaba na yanzu Alhaji Sanusi Lamido Sanusi Na 2 yake kokarin dorawa daga inda ya gada. Allah Ka Kara karfafarsu, ameeeeen. ! ! ! Ya kamata kowanne Musulmi ya yi kyakykyawar addu'a, ga mai martaba Sarkin Musulmi da sauran Sarakun Musulunci baki daya, allah Ya kara musu Lafiya, ya ba su ikon hada kan musulmai, tare da shugabancin Najeriya, baki daya ameeeeeen ! ! ! ! Allah Ka kara haskaka kabarin Marigaji Mai martaba, Alhaji Dr. Ado Bayero, ammeeeeeeen ! !


Allah Madaukain Sarki Ya Ce: "Ya ku wadanda kuka ba da gaskiya, an wajabta Azumi a kanku kamar yadda aka wajabta shi a kan wadanda suka gabace ku, (An Yi Haka Ne) Don ku yi tsoron Allah. 'Yan kwanaki ne kidayayyu; wanda kuwa yana cikin tafiya, (Ya Sha Azumi) sai ya cika adadin abin da ya sha daga wasu kwanaki. ! ! ! ! ! Kuma fansa ta ciyar da Miskini tana kan wanda suka sha tare da ikon yin sa (Da Kyar). ! ! ! Wanda Ya kara (Ita Fansar) don samun lada wannan shi fi masa Alkhairi. ! ! ! ! ! Amma kuma ku yi Azumin (Shi Ya Fi) Alkhairi a gare ku idan kun kasance kun san (Haka, To Sai Ku Aikata Shi). (Wannan Shi Ne) watan Azumi wanda aka saukar da Alqur'ani a cikinsa, don shiriya ga mutane da (Ayoyi) Mabayyana na shiriya da rarrabewa tsakanin karya da gaskiya. ! ! ! ! ! (Wanda Ya Rayu Cikinku Har Zuwa Watan Ko Sai Ya Azumce Shi, Kuma Wanda Ya Kasance Marar Lafiya Ko A Cikin Tafiya Sai Ya Yi Adadin Wasu Kwanakin (Dai-dai Yawan Wadanda Ya Sha). ! ! ! ! ! Allah Yana nufin sauki ne a gare ku, kuma ba Yana nufin wahalar da ku ba ne, don ku cika adadin kwanakin don kuma ku girmama Allah A bisa abin da Ya Shirye ku, ko kwa gode wa (Ni'imominsa). ! ! ! ! ! Idan bayina suka tambaye ka game da Ni tYa Muhammadu S.A.W. Ka Ce Da Su): Hakika Ni a kusa nake, ina amsa addu'ar mai addu'a idan ya roke Ni; saboda haka su nemi biyan bukata gare Ni, kuma su ba da gaskiya da Ni don su shiriya. ! ! ! ! ! An halatta muku tarawa da matayen ku a daren Azumi; Su sutura ne a gare ku, ku kuma sutura ne a gare su. Ubangiji ya san cewa hakika kun kasance kuna ha'intar kanku, sai Ya kar6i tubanku kuma Ya yafe muku (Ba Tare Da Ya Yi Muku Azaba Ba); To yanzu ku rungume su, ku nemi abin da Allah Ya halatta muku, kuma ku ci ku sha har sai farin kwalle ya bayyana a gare ku daga bakin kwalle na Alfijir (Watau Har Izuwa Fitowar Alfijiri); sannan ku cika Azumi zuwa dare. Kada ku rungume su idan kuna lazimtar idaba cikin Masallatai. Wadancan iyakokin Allah Ne, to kada ku kusance su. Kamar haka Alllah Yake bayyana ayoyinsa ga mutane don su tsorata". ! ! ! ! ! Allah Ta'ala Ya ce: "Hakika. Mu Muka saukar da shi a cikin dare mai albarka. Hakika Mu Mun kasancce masu garkadi". ! Suratul Duhani Aya Ta 2. ! ! ! ! ! Allah Ta'ala Ya Ce: "Da masu Azumi maza da mata, da masu kiyaye tsiraicinsu maza,da mata masu kiyaye tsiraicinsu, da maza masu ambaton Allah da Yawa, da Mata masu ambaton Allah da yawa, dukkaninsu Allah Ya yi musu tanadin Gafara da Lada mai girma". ! Suratul Ahzab Aya Ta 35-36. ! ! ! ! ! Allah Ta'la Ya Ce: "Ku ci ku sha, kuna masu farin ciki, saboda abin da kuka gabatar a kwanakinku da suka wuce (Na Duniya) ! ! Suratul Hakati Aya Ta 24. ! ! ! ! !




Make a free website with Yola