"DABI'U NA GARI" .
Al'amarin kyawawan dabi'u al'amari ne na 'yan Adam da aka yi tarayya a kansa tsakanin mutane gaba dayansu da dukkan sabanin addinansu da nisan yankunanasu da kuma yarukansu. Mutum yana rayuwa a jama'a ne da a cikinsu akwai na nesa, da na kusa, da karami, da babba, da mace, da namiji, da mai neman sani, da malami, kuma da mai kasuwanci, da maras aiki. Mutum yana bukatar abubuwan da ta hanyar su ne zai kiyaye mu'amala da sauran mutane don cimma gurin rayuwarsa da bukatunsa kamar yadda Allah ya yi umarni. . Don haka ne ma kyawawan dabi'u suka zama tsani domin nuna yadda ya kamata a yi mu'amala da wasu, da kuma yadda za a yi mu'amalar mutum tare da wani mutumin a bisa ka'idar "Yin mu'amala da mutane kamar yadda kake so a yi mu'amala da kai". Ko kuma "Kamar yadda ka yi za a yi maka" . Saboda haka mutum ba ya wadatuwa gabarin wannan dabi'a da zata kare ayyukansa, ta kuma tsarkake tunaninsa, da kuma bayar da gudummuwar nisantar da kai daga ayyuka marasa kyau, domin ba komai ne ya sa aka halicci mutum ba sai domin ya samu daukaka zuwa ga kamala, da kuma gina al'ummar da adalci da taimakekeniya zasu zama su ne suke jagorantar ta domin kariya daga zalunci da fasadi. . Wannan shi ne abin da ake kira "Kyawawan dabi'u wato Akhlak" Wanda ya kasu zuwa na nazari da na aiki. Ta wani bangaren kuma wajibi ne a nisatar da kai daga karya, da ha'inci, da hassada, da riya, da rudin kai, da jiji da kai, da mugun kuduri, da giba, haka nan wajibi ne a siffantu da gaskiya, da amana, da burin alheri ga juna, da sauransu na daga kyawawan dabi'u da ya zama wajibi ne a kan mutum ya san su, kuma ya san munananta da kyawawanta, wannan duk ana cewa da shi Ilimin Kyawawan dabi'u na nazari. . Sannan sai a siffantu da su a rayuwa a aikace tare da iyalai, da 'yan'uwa, da makwabta, da wadanda suke gefe, wannan shi ne ake kira Ilimin Kyawawan dabi'u na aiki. . Da mun kula mun yi la'akari da zamu samu cewa mafi yawancin mutane da suka siffantu da Kyawawan dabi'u su ne annabawa, musamman Annabinmu mafi girma Muhammad (s.a.w) ta yadda ya zama yana daga sababin aiko shi, shi ne domin ya cika manyan dabi'u kamar yadda shi da kansa (s.a.w) ya shelanta, ya kasance yana siffantuwa kafin a aiko shi da mai gaskiya amintacce; saboda gaskiyar zancensa da aiki da amana har Allah madaukaki ya yabe shi da cewa: "Lallai kai kana da kyawawan dabi'u masu girma" . . Ashe kenan kyawawan dabi'u suna da muhimmanci mafi girma, kuma suna daga siffofin Annabawa, kuma an yi tarayya a tsakanin mutane a cikinsu, sai dai cewa mafificiyarsu kuma mafi girmansu sun tabbata ne kuma an san su ne saboda aiko fiyayyen 'yan Adam Annabi Muhammad (S.A.W). . Wannan makala da ta kunshi sanin kyawawan halayen musulunci, an rubuta ta ne domin dan Adam musamman musulmi ya samu tsinkayo game da dabi'un da musulunci ya zo da su, wacce yake wajibi ne ya san ta ya kuma siffantu da ita ya kuma yi aiki da ita, musamman a wannan zamani da mafi yawancin mutane suka koma tamkar dabbobi, zalunci da keta suka mamaye ko'ina, aka rasa aminci da amana, aka kuma bata sunan musulunci, ta hanyar mutane da suka karkace suka fari sabon kire ga musulunci, suka yi barna da sunan musulunci, wanda musulunci ya barranta daga garesu. . Musulunci addinin kyawawan dabi'u ne da soyayya da aminci da mutumtaka, kuma addini ne da yake maganin cututtukan rai, yake kuma fuskantar da mutum zuwa aljanna. . Muna rokon Allah madaukaki mai rahama ya sa mu dace da bin dabi'un musulunci, ya kuma ba mu ikon bayyanar da su ga mutane a wannan gajeriyar makala, ta zama kofa ga kowane mutum; domin shiga da sanin kyawawan dabi'un musulunci. Kuma muna rokon Allah ya karbi wannan aiki da kuma neman addu'a daga muminai.
.
Dangane da akhlak na musulunci muna ganin yana da manyan madogara na asasi guda biyu manya, sune:
1-Hankali
2-Annabin rahama (s.a.w) da Ahlul baiti (A.S)
.
1- Hankali
Hankali; Ana auna ayyuka da hankali ne, kuma da shi ne mutum yakan kai zuwa ga sa'ada da kamalar rayuwa ta lahira, da hankali ne muke riskar dalilin halitta, da kuma riskar abubuwa masu daraja, muke kuma kokari zuwa ga mafi kyau ma fi wanzuwa, da shi ne muke neman tafarkin sani, da hanyoyin ibada, Imam Assadik (a.s) ya ce: "Mafi kamalar mutane hankali shi ne mafi kyawunsu dabi'a" .
.
Dogaro da wannan hadisin muna iya cewa; hankali na aiki shi ne abin nufi, ba hankali na nazari ba, in Allah ya yarda idan na kammala littafina wanda yake magana kan kashe-kashen hankali da matsayin kowanne, to a nan mun kawo bayani game da hankali dalla-dalla.
.
Hankali a nazarinmu shi ne madogara ta asali na kyawawan dabi'u, idan aka rasa shi sai dabi'ar halin dabbanci ta mamaye mutum.
.
2- Annabi Mai Girma Da Ahlul Bait (a.s)
Annabi mai girma ya zo ne domin ya tsarkake mu ya cika mana kyawawan dabi'u yayin da yace: "Kawai an aiko ni ne domin in cika kyawawan dabi'u" .
.
Shine mafi kamalar mutane, kuma babu wani daga halittu da ya kai inda ya kai, shi ya sanya ubangiji madaukaki ya fada yana mai yabonsa: "Lallai kai kana kan halayen dabi'u masu grima ne" .
.
Abin da ya hau kanmu shi ne mu yi riko da kyawawan dabi'unsa, mu yi koyi da shi domin shi ne abin koyi kuma madogara garemu a kyawawan dabi'u, har ma a kowane fage.
.
Amma Ahlul Baiti (a.s) su ne wadanda suka gaji ilimn annabawa da na karshensu Muhammad (s.a.w), kuma mutane sun gani kuma sun ji kyawawan dabi'un alayensa (a.s) wancce take iya tuna musu kyawawan dabi'unsa (s.a.w).
.
Da sannu zamu ambaci wasu daga kyawawan dabi'unsu a wannan littafin namu; Daga ciki;
"Ya zo cewa imam Hasan da Husain (a.s) sun wuce wani tsoho yana alwala bai iya ba, sai suka yi kamar suna 'yar jayayya a kan cewa; wanene yafi iya alwala a cikinsu, wannan kuwa sun yi haka ne domin su koya masa yadda ake yin alwala, sai kowanne ya ce kai ne ba ka kware ba sosai,
.
Sai suka ce: ya kai wannan tsoho yi mana hukunci, sai kowannensu ya yi alwala sannan sai suka ce: Waye a cikinmu ya fi iyawa?
.
Sai ya ce: Ai duk kun iya alwala, sai dai wannan tsoho jahili shi ne bai iya ba, yanzu kam ya koya daga gareku" .
Lura da yadda Ahlul Bait (a.s) suka shiryar da wannan tsoho domin ya zama mana darasi a wajan yadda ake mu'amala tare da manyan mutane.
Gaskiya
Gaskiya ita ce; yin daidai da hakikanin al'amari a zance, da aiki, ko nufi, kuma tana daga cikin siffofi madaukaka da suke da falala mai yawa wadanda ya wajaba ga mutum ya siffantu da su. Ayoyin kur'ani da ruwayoyi masu yawa sun zo game da yabon masu gaskiya.
.
Kashe-Kashen Gaskiya
"Gaskiya ta zance; kamar bayar da labarin hakikanin abin da ya faru a magana
.
"Gaskiya ta niyya da nufi; kamar tsarkake zuciya da aiki don Allah, ko nufin aikata alheri da gaske
.
"Gaskiya a ayyuka kamar cika alkawari da daukar matakai na daidai
.
Gaskiya tana daga cikin abubuwan da ake kimanta mutum da ita a wajan Allah (s.w.t), imam Sadik (A.S) yana cewa da mu: "Kada ku yaudaru da sallarsu, ko da azuminsu, saudayawa mutum yakan saba da salla da azumin har idan ya bar su sai ya ji ba dadi, amma ku jarrabi mutane da gaskiyar magana da bayar da amana ".
.
A wata ruwayar yana cewa: "Wanda harshensa ya yi gaskiya aikinsa zai tsarkaka" .