TUBBA’UL AWWAL YAYI BISHARAR ZUWAN ANNABI MUHAMMADU S.A.W.
Tubba’ul Awwal wani Babban Sarki ne da akayi a kasar Yaman, Yaci Duniya Da Yaki Amma Shi Musulmi ne, Tsakanin Sa Da ANNABI Muhammadu S.A.W. Shekara Dubu.
Ya Taso Yana Yakin Kasashen Duniya Har Yazo Garin Makka Yayi Niyyar Ya Yakeso Sai Manyan Malaman Da suke Tare Dashi Suka Hanashi Domin cewa Anan ne Za’a aifi Annabi Karshen Zamani.
Anan Yayi Farin ciki Sosai Daga Nan Ya Tafi Garin Madina.
Sai Aka Fada Masa Cewa Annabin Karshen Zamani Zayyi Hijira Ya Dawo Wannnan Gari Kuma A cikinta Zaiyi Wafati.
Sai Ya Sami Bayi Maza Guda Dari Hudu Da Bayi Mata Guda Dari Hudu (400) Ya Auraddasu Ga Junansu Kuma Ya Gina Masu Gidaje Domin Ko Zuri'arsu Sun Riski Annabi Karshen Zamani.
Sannan Ya Gina ma Dansa Gida Anan Garin Madina Yace Ya Zauna.
Sannan Ya Rubuta Wasika Ta Musamman Aciki Yana Yabon Annabi Muhammadu S.A.W. Kuma Yana Burin Da Ace Ya Riski Annabi Muhammadu S.A.W. Da Ya Taimaka Masa Kamar Yadda Sahabinsa Aliyu Zai Taimaka Masa.
Amma Annabi S.A.W. Ya Shaida Tun Daga Yau Tubba’u Ya Sallama Masa Akace Daga Ranar Da Ya Rubuta Wasikar Zuwa Ranar Da Annabi Yayi Hijira Shekara Dubu(1000).
To Sayyidina Abu Ayyuba Al Ansary R.A. Jikansa Ne Domin Lokacin Da Annabi S.A.W. Yayi Hijira Wasikar Tana Hannunsa ne, Kuma Annabi S.A.W. Ya Sauka Agidansa Domin Nan ne Tubba’u Ya Gina Domin Annabi S.A.W. Shekara Dubu Tsakani.
Kaji Masoya Annabi A.S. Na Tun Tuni.
KA'ABU YAYI BISHARAR ZUWAN ANNABI MUHAMMADU S.A.W.
Sayyidina Ka’abu Yana Daga Cikin Kakannin Annabi Muhammadu S.A.W.
Ya Kasance Duk Ranar Juma’a Yana Tara Mutane Yana Basu Bayanai akan Annabin Karshen Zamani.
Har yakanyi masu Ishara da cewa Acikin su ne Allah zai bayyanar dashi.
Sun Kasance Tun a wancan Lokacin suna Tawassuli Da Annabi Muhammadu S.A.W
ANNABI BULUQIYA YAYI SHAUKIN ANNABI MUHAMMADU S.A.W.
Wannan Annabi Mai Suna Buluqiya Yana Daga Cikin Annabawan da Suke Karkashin Annabi Musa A.S.
Ya sami Siffofin Annabin mu acikin Littafan Annabwa, Tun Daga Lokacin Ya Fara Shaukin Son Ya Hadu Da Annabi Muhammadu S.A.W.
Amma Allah Bai Sanar Dashi Lokacin Da Annabi S.A.W. Zai Bayyana Ba.
Sai Ya Shiga Duniya Domin Neman Labaran Bayyanan Annabi Muhammadu S.A.W.
Yanata Tafiya Har Yakai Wajen Dutsen Qaaf (Itace Dutsen da Ya Kewaye Duniya) Ya Hadu Da Wani Gari Na Aljannu, Ya Tambayesu Game Da Labarin Bayyanar Annabi Muhammadu S.A.W. (Baisamu ba) Sukace sai dai yayi gaba.
Yaje Gab Wata Duniya babu komai Sai macizai (Nan Ma Yaga Wasu halittu masu ban tsoro) Ya Tambayesu Game da Labarin Bayyanar Annabi Muhammadu S.A.W. Bai Samu Labari ba.
A takaice dai bai samu Wani Karin Bayani Ba Har sai da yaje Wata Duniya: Anan Allah Ya Hadashi Da Annabi Hadir A.S.
Ya Fada Masa Cewa: "Annabi Muhammadu S.A.W. Zai Bayyana Amma Lokacinsa Bayyi ba, Saura Shekara Kusan Dari Takwas.
Yayi ta Kuka Na Rashin Saduwa da Annabi MUHAMMADU S.A.W.
Sai Sayyidina Hadir Yasanya Karama Yana Dafa Kansa Sai Annabi Buliqiya Ya ganshi a kofar Gidansa Ya dawo Cikin Second guda.
Anan Allah Ya Zabeshi Ya Bashi Annabta.
Sabida Soyayyar Da Ya Nuna Ma Annabi Muhammadu S.A.W.
ALLAH YA KARRAMA WANDA YA KARRAMA ANNABI MUHAMMADU S.A.W. A JAMA'AR ANNABI MUSA A.S.
A Zamanin Annabi Musa A.S. Akwai Wani Daga Cikin Jama'arsa, Bashi da yawan Ibadu Sai Yawan Sabo.
Amma Ya Kasance Duk idan Yazo Karatun Littafin ATTAURA Zaiga Wajen Da Aka Rubuta Sunan Annabi Muhammadu S.A.W. Sai Ya Sumbanta Da Niyyar Soyayya.
Kawai Sai Ya Rasu.
Kowa Yaki Yaje Yayi masa Sallah har Annabi Musa A.S. Yaki Zuwa, Sabida Ansan cewa Shi Fasiqi ne.
Sai Allah Ya Turo Mala’ika Jibrilu A.S. Wajen Annabi Musa A.S. Cewa Yaje Yayi Masa Sallah Sabida Ya Kula Da Masoyi na Annabi Muhammadu S.A.W.
ALLAH YAYI MASA GAFARA SABODA ANNABI MUHAMMADU S.A.W.
ANNABI MUSA A.S. YAYI BURIN KASANCEWA A CIKIN AL'UMMAR ANNABI MUHAMMADU S.A.W.
Annabi Musa A.S. Lokacin Da Yaga Martaba da darajoji Na Ummatu Muhammadin S.A.W. Sai Ya ROQI Allah Akan Ya Sanyashi CIKIN Wannan Al’umma.
Sai Allah Yace masa Ya Rike Abinda Allah Ya Bashi Ya Zamo Masu Godema Allah.
Maulan Mu Sheikh Ibrahim Inyass R.A. Yana cewa
ﺗﻤﻨﻰ ﻛﻠﻴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﻟﻮ ﻛﺎﻥ ﻭﺍﺣﺪﺍ * ﻣﻦ ﺃﻣﺔ ﺧﻴﺮ ﺍﻟﺨﻠﻖ ﺫﺍﻙ
ﻣﻘﺎﻟﻪ