Welcome to my site................................

ALLAH YA HALLAKA AS HABUL FILI.

Lokacin da Sarki Abrahata Yaga Abdul Mudallib Ya Tsorata Da Kalaman Da Ya Fada Masa, Sanna Kuma Bokayensa Sun Bashi Labarin Cewa a Wannan Garin ne za’a Haifi Annabin Karshen Zamani, Sai Ya Tsorata.
Amma Duk Da Haka Baisa sun janye Daga Niyyarsu ta Rushe Dakin Ka’aba ba.
Sai Suka Tashi Manyan Giwayennan da suna Korasu bangaren dakin Ka’aba, Giwayen sukaki.
Acikinsu akwai Wani Babban Giwa Sunansa MAHMUDU, Sai Sarki Zu Nafarain Yaje Kunnin Giwan Ya Fada Masa cewa: “KAJI TSORON ALLAH , KA SANI AWANNAN GARIN NE ZA’A HAIFI ANNABIN KARSHEN ZAMANI, KUMA KA SANI INDAI HAR KA RUSHE WANNAN DAKIN ALLAH BAZAI BARKA BA KUMA KO A LAHIRA BAZA’A GANKA BA”.
Wannan Giwar Ya juya da baya ya gudu, Sai sauran Mutane suka Hau sauran Giwayen Suka Nufi Dakin Ka’aba.
Take Nan Allah Ya Turo Da Manyan Tsuntsaye Suka Dakko Duwatsun Wuta daga Gidan Wutan Jahannama.
A kowanne Tsakuwa akwai sunan ko wani kafiri a cikinta.
Idan Tsakuwar ya sauka akan Kafiri Zai Huda Tun daga Tsakiyar Kansa Har Giwan ko Dokin.
Duka Suka Soye, suka Zama Labari Saboda Sunja Da Dakin Allah.
Toh Yaya Zatonka Ga Wanda Kullum Baida aiki sai tauye Darajar Annabi Muhammadu S.A.W. Da Sukarsa.

IYAYEN ANNABI MUHAMMADU S.A.W. SAYYIDINA ABDULLAHI DA SAYYIDA AMINA.
Bayan An sami amincewar Kowa akan maganar Auren Haske da Kuma Wanda Zata Dauki Hasken Sayyidina Abdullahi da Sayyida Amina Alaihimussalatu Wassalam.
Aka Sanya Rana Domin Daurin Aure
(Alhamdulillah).
Allah Ya Kara Ma Sayyida Amina Kyau Da Haske Da Kamshi Fiye da Duk wata Mace alokacin (Domin shirin da ake mata Na Daukar Babban Haske Na ANNABI MUHAMMADU S.A.W.).
Aka Daura Auren SAYYIDINA ABDULLAHI DA SAYYIDA AMINA.
ALLAH MUNA TAWASSULI DA WANNAN AURE ALLAH DUK WANI MAI DAMUWA A CIKIN MU, ALLAH KA YAYE MASA, ALLAH KA BAMU DUKKAN ALHAIRAI, ALLAH KA KIYAYEMU DUKKAN SHARRUKA, ALLAH KA FITAR DAMU KUNCI DON ARZIKIN IYAYEN ANNABI MUHAMMADU S.A.W. ANNABI MUHAMMADU S.A.W. SAYYIDINA ABDULLAHI DA SAYYIDA AMIN.

SAMUN CIKIN ANNABI MUHAMMADU S.A.W.

Ranar Da za’a Sami cikin Annabi Muhammadu S.A.W. Ya Kasance ne Ranar Alhamis Daren Juma’a Na biyu Cikin Watan Rajabul Fardu.
Sayyidina Abdullahi Yana Kwance a Dakin Ka’aba Sai Yaji an tashe shi, Da Ya tashi zaije Gida Sai Yaga Wani Korama Na Haske a Gabansa, Sai Yaji ana cewa Ka Shiga Cikon wannan Ruwan Kasha kayi Wanka, Domin Yaune aka Kaddara Matarka Zata Samu ciki.
Bayan Yasha Wannan Ruwan yayi wanka, sai Ya Kara Kyau akan kyau da haske.
Yana Kan hanya Sai Ya Hadu Da Wata Mata Bayahudiya Masaniyace akan dukkan Taurari Malamace sai tace masa: “Abdullahi Inaso Ka Fada min Ko nawa Zan baka Acikin darennan Ka Aureni koda Da Safe Zaka Sakeni Na Yarda!!”.
Sai Yace mata ai bai yarda ba, matarsa ma tana jirarsa yanzu haka! Ita Waccan bayahudiyar wai tana kwadayin wannan haskenne na Goshinsa Kuma Taga Alama Awannan Ranar Za’a Sami cikinsa S.A.W.
A can Gida Itama Sayyida Amina Tana Zaune Tana Jiran Mijinta Ya dawo sai Taga Wani Korama A tsakar gida akace mata ta shiga tayi wanka tasha itama.
Da Tasha Ta Kara Kyau da Haske FAL FAL.
Da Ya dawo gida, sukaga gidan Ya Cika da haske, kowanne A cikinsu yana haske.
A wannan Daren ne Allah Ya Tara Dukkan Mala’iku Yace Suyi Sahu Sahu Domin Yaune Alkawarin Allah Ta Cika (INNALILLAHI WA'INNA ILAIHIRRAJI'UN).
A daren Ya Sadu Da ita, Hasken Ya Koma Jikinta.
Da Gari ya waye akaga haske ya koma goshinta.

WAFATIN SAYYIDINA ABDULLAHI.

Bayan an samu Cikin da Babu Kamarsa da Wajen Uban da Babu Kamarsa da Uwar Da Babu Kamanta.
Sayyiduna Abdul Mudallib yayi farin ciki da Murna, Sai Yace: "Tun Yanzu zamu fara shirin Haihuwar Wannan Babban Haske".
Yace ma Sayyiduna Abdullahi Yazo yaje Madina Domin Kasuwanci kuma daga Nan A siyo Kayan abinci da Za’a rabama Alhazai da Kuma Shirin Haihuwan Annnabi Muhammadu S.A.W.
Sayyiduna Abdullahi Ya tafi Zuwa Madina Yana Dawowa Hanya a Garin Abwa’I Yayi Wafati Lokacin Annabi S.A.W. Yana da Shekara Biyu a Ciki SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM.
Labari Ya iso Garin Makka na Wafatin Sayyiduna Abdullahi (Babu Dadi).
Sayyiduna Abdul Mudallib Yace: Nayi Alqawarin duk abinda Uba yakanyi ma Dansa Zanyi ma Wannan Dan dake ciki Fiye da hakan Insha Allah, zan zamo masa Uba. Kuma Hakan akayi.
Daganan Ana ta Zuwa Barka Zuwa wajen Sayyida Amina, Tun daga Kan Mala'iku, Annabawa, Aljannu, Ruhanai, Dabbobi da Sauran Halittu. DOMIN NUNA FARIN CIKIN SU NA SAMUWAN ANNABI MUHAMMADU S.A.W.

ALAMOMIN BAYYANAR ANNABI MUHAMMADU S.A.W.
Bayan Komawar Boka Sadihu Gida, Can Gidan Mulkin KISRA Sai Su kaga Ya Tsage Goma Gida Goma Sha Hudu (Wannan Ginin Kuwa Anyishi Da Manyan Duwatsu Kuma Yanada Kauri Na wajen Zira’i Ashirin) Sai Sunata Mamaki.
Ana Cikin Wannan Halin acikin Daren Shi Kuma Wazirin KISRA yayi Mafarki Raquma 14 suna Jan Dawakai Sha Hudu.
Ya Farka Da Safe Sai Kuma sukaji Labari Yazo cewa Kogin SAWATA Ya Qafe (Tekuce da suke bautama Na Tsawon Shekaru Bata Taba Qafewa ba).
Sai Kuma Labari Yazo cewa Tekun SAMAWATA Ta Bubbugo (ita kuma Kuma Shekara da Shekaru Ruwan cikinta Ya Qafe).
Sannan akwai Wata Wuta Da suke Bautamawa Shekara da Shekaru Bata Taba Mutuwa ba Kawai Suka Wayi Gari Wutar Ta Mutu Gaba Daya.
Hankali Ya Tashi Sai Waziri Mubizan Sukayi Shawara Da Sarki akan A rubuta Wasika zuwa ga Boka SADIHU Domin A sami Bayanan Wadannan Abubuwa da suka Faru.
Boka Sadihu Yace;
1. Tsagewar Katangara Kisra Goma Sha Hudu Ishara Ce Na Karewar Mulikn Sarakunan Kisra Bayan An sami Sarakuna Sha Hudu.
2. Raquma Sha Hudu Da suke jan Dawakai Sha Hudu, Bayani ne akan ANNABIN KARSHEN ZAMANI zai bayyana ne ciki Larabawa kuma Sune Zasu Karar Da Mulkinku bayan an sami Shekara Sha Hudu Mulkin Kisrah Zai Koma Hannunsa S.A.W.
3. Qafewar Teku, da Bayyanar Teku da Kuma Mutuwar Wuta, Alamomi ne na Bayyanar Wanda Zai Rushe Karya, A Bar Bautama Kowa Sai Allah.
Boka Sadihu Yana Gama Rubuta masu wannan Wasika Ya Fadi Ya Mutu Yana Mai Bakin cikin Bayyanar Annabi Muhammadu S.A.W.
Allah Ka Kiyayemu.


WATAN HAIHUWAR MA'AIKI S.A.W. YA TSAYA.
A L H A M D U L I L L A H x 3.
Bisharorori Sun Karu Lokacin da AKA shiga cikin Watan Rabi’ul Awwal Bayan Zuwan Annabi Isa A.S.
SAYYIDA AMINA A.S. MAI ALFARMA tace: "Daren Farko Taji Farin Cikin Ta Ya Karu, Lafiyarta Ya Karu, Zuciyarta ta cika da Haske da Farin ciki.
Dare Na Biyu Tace aka kara yaye damuwar Zuciyarta, aka yi mata bishara da cewa An Daga Darajarta akan Matan Duniya Baki Daya.
Dare NA Uku Sai Taji Mai Kira yana Kira Yana Cewa: “Ku Sani Fa Wanda Zai zo Da Sakon Allah Na Kalmar Godiya Ya Kusa Bayyana a wannan Duniya, Haihuwarsa Ya Kusa”.
Dare Na Hudu Aka Yaye mata Hijabai Tana jin Mala’iku Sunata Bishara a Tsakaninsu suna Tasbihi Da Godema Allah Tanaji Kuma Tana Ganinsu.
Dare Na Biyar Acikin Barcinta Sai Taga Annabin Allah Annabi Ibrahim A.S. Yace mata “Ya Aminatu Hakika Kin Daukaka domin Allah ya fifitaki Ya Baki Wannan Alhairi”.
Dare na Shida Sayyida Amina A.S. Taga An Cika Sammai da Kassai Da Haske Da Annurai Ko Ina Haske Taurari sun Kara Haske, Wata Ya Kara Haske.
Dare na Bakwai Aka Kara yaye mata Hijabai Daga Dakinta Tana Hango Mala’iku Masu Tasbihi A Fadar Allah Sunata Farin Ciki.
Dare Na Takwas Sai Taji Wani Mala’ika Yana Cewa: “Ya Sayyida Aminatu Hakika Haihuwar Hasken Hasken Ya Kusanto Saboda Haka Farin Ciki Ya Tabbata A Gareki”.
Dare Na Tara Taji ana yi mata wasu Kalamai masu Dadi “An miki Bishara da Sa’adah na har abadah”.
Dare Na Goma Farin cikinta Ya Kara Karuwa (YA RASULALLAH).
Dare na Sha Daya Babu Wani Abu da yake damunta Domin Zuciyar ta gama cika da Haske.
Da Izinin Allah A Rubutu Na Gaba Zamu Kawo Yadda Haihuwar Ta Kasance A Dare Na Sha Biyu Ga Watan Rabi'ul Awwal Insha Allah.
Allah Muna Yin Tawassuli Da Sayyida Amina: Allah Albarkacinta Allah Ka Cikamu Da Haske Na Soyayyar Annabi Muhammadu S.A.W. Allah Ka Yaye Ma Dukkan Damuwarmu. Allah Ka Faranta ranmu. Allah Kaso mu kuma Ka Zabemu ka Daukakamu. Allah Ka Saka ma Shehunmu Da Alhairi don Arzikin Sayyida Amina A.S. HAIHUWAR MA'AIKI S.A.W. YA TSAYA.
A L H A M D U L I L L A H x 3.
Bisharorori Sun Karu Lokacin da AKA shiga cikin Watan Rabi’ul Awwal Bayan Zuwan Annabi Isa A.S.
SAYYIDA AMINA A.S. MAI ALFARMA tace: "Daren Farko Taji Farin Cikin Ta Ya Karu, Lafiyarta Ya Karu, Zuciyarta ta cika da Haske da Farin ciki.
Dare Na Biyu Tace aka kara yaye damuwar Zuciyarta, aka yi mata bishara da cewa An Daga Darajarta akan Matan Duniya Baki Daya.
Dare NA Uku Sai Taji Mai Kira yana Kira Yana Cewa: “Ku Sani Fa Wanda Zai zo Da Sakon Allah Na Kalmar Godiya Ya Kusa Bayyana a wannan Duniya, Haihuwarsa Ya Kusa”.
Dare Na Hudu Aka Yaye mata Hijabai Tana jin Mala’iku Sunata Bishara a Tsakaninsu suna Tasbihi Da Godema Allah Tanaji Kuma Tana Ganinsu.
Dare Na Biyar Acikin Barcinta Sai Taga Annabin Allah Annabi Ibrahim A.S. Yace mata “Ya Aminatu Hakika Kin Daukaka domin Allah ya fifitaki Ya Baki Wannan Alhairi”.
Dare na Shida Sayyida Amina A.S. Taga An Cika Sammai da Kassai Da Haske Da Annurai Ko Ina Haske Taurari sun Kara Haske, Wata Ya Kara Haske.
Dare na Bakwai Aka Kara yaye mata Hijabai Daga Dakinta Tana Hango Mala’iku Masu Tasbihi A Fadar Allah Sunata Farin Ciki.
Dare Na Takwas Sai Taji Wani Mala’ika Yana Cewa: “Ya Sayyida Aminatu Hakika Haihuwar Hasken Hasken Ya Kusanto Saboda Haka Farin Ciki Ya Tabbata A Gareki”.
Dare Na Tara Taji ana yi mata wasu Kalamai masu Dadi “An miki Bishara da Sa’adah na har abadah”.
Dare Na Goma Farin cikinta Ya Kara Karuwa (YA RASULALLAH).
Dare na Sha Daya Babu Wani Abu da yake damunta Domin Zuciyar ta gama cika da Haske.
Da Izinin Allah A Rubutu Na Gaba Zamu Kawo Yadda Haihuwar Ta Kasance A Dare Na Sha Biyu Ga Watan Rabi'ul Awwal Insha Allah.
Allah Muna Yin Tawassuli Da Sayyida Amina: Allah Albarkacinta Allah Ka Cikamu Da Haske Na Soyayyar Annabi Muhammadu S.A.W. Allah Ka Yaye Ma Dukkan Damuwarmu. Allah Ka Faranta ranmu. Allah Kaso mu kuma Ka Zabemu ka Daukakamu. Allah Ka Saka ma Shehunmu Da Alhairi don Arzikin Sayyida Amina A.S.

BISHARAR DA MANYAN ANNABAWA SUKAYI NA SAMUN CIKIN ANNABI MUHAMMADU S.A.W.
Watan Farko Wato Watan Rajab, Annabin da Ya Fara Zuwa Wajen Sayyida Amina A.S. Ya Gaida Annabi Kuma Yayi Mata Bishara Shine: ANNABI ADAMU A.S. Yazo Yana Haske Ya Kamshi Ya Duka a gabanta Yana cewa: “Barka Da zuwa Ya Shugabanmu Annabi Muhammadu S.A.W. Nazo ne In Gaisheka Kuma In Sallama maka Ya Rasullah”.
Sayyida Amina A.S. Tace Ban ganeka ba, Wanene kai? Sai Yace: Ai nine “Annabi Adamu Abul Bashar nazo ne inyi masa Muba’ya’a” Kuma Ina Yi miki Bishara cewa :”Kin Sami Cikin Shugaban Halittu Gaba Daya”.
Sayyida Amina Tace Annabi S.A.W. Yana Ciki amma Ya amsawa Annabi Adamu A.S. Sallama Kuma Ya Sanya Masa Albarka.
Kaji Wanda Annabawa ma suke Neman Albarkansa ANNABI MUHAMMADU S.A.W.
A WATA NA BIYU Watan Sha’aban ANNABI SHISU A.S. Sai Ga Wani Annabin Yana Haske Yana Kamshi Shima Ya duqa Gaba Sayyida Amina yace: “ASSALAMU ALAIKA YA RASULALLAH”.
Sayyida Amina A.S. Tace: “Ban Ganeka Ba” Sai Yace: "Ai nine Annabi Shisu A.S. Nazo ne inyi Muba’ya’a agareshi Kuma Inyi miki Bishara “Kin sami Cikin Mai Tawili Da Hadisi”.
Shima Yaji Muryar Annabi S.A.W. Ya Sanya Masa Albarka. Allah Kasa Annabi S.A.W. Yasanya Mana Albarka Da Wannan Maulidi Da Mukeyi.
WATA NA UKU Watan Ramadan Zuwan ANNABI IDRISU A.S.
Yazo Yana Haske Yana Kamshi Ya Duqa Gaban SayyidaAmina Yace:
“ASSALAMU ALAIKA YA NABIYULLAH”. Sayyida Amina A.S. Ta Tambayeshi Wanene Kai?. Sai Yace: "Nine Annabin Allah Annabi Idrisu nazo inyi miki Bishara Da Samun Wannan Ciki Mai Albarka Kuma Nazo ne In Sallama masa.
Kuma Ina yi miki bishara Kin Sami Cikin “LU’U LU’U MAI TSADA”.
“Ina Maki Bishara Domin Kin Sami Cikin”.
Annabi S.A.W. Ya Amsa Kuma Yasa Masa Albarka.
Allah Kayi mana Albarka Albarkacin Albarka shine Annabi Muhammadu S.A.W.
WATA NA HUDU Watan Shawwal ANNABI NUHU A.S. Ya sami Sayyida Amina A.S.Yana Kamshi Yana Haske Ya duqa yace: “ASSALAMU ALAIKA YA HABIBULLAH”.
Nazo ne In sallama maka Ya Rasullah, Kuma Ina Yi miki Bishara da cewa: “Kin sami Cikin Ma’abocin Nasara Da Fatahohi”.
Annabi S.A.W. Ya Amsa Kuma Ya Sanya Masa Albarka.
WATA NA BIYAR Watan Zul~Qada ANNABI HUDU A.S. Yana Haske Ya duqa a gaban Sayyida Amina A.S. Yace: “ASSALAMU ALAIKA YA SAFWATULLAH”.
Nazo ne nayi Muba’ya’a Kuma Inyi Miki Bishara cewa: “Lallai Kin sami Cikin Fiyayyen Duk Abin Haihuwa”.
Wadannan fa dukansu Annabawa ne
Kaji Yadda Suke Neman Fada wajen Annabi Muhammadu S.A.W. To Yaya Kai? Yaya Ni? Yaya Ke?.
WATA NA SHIDA WATAN ZUL~HAJJ Zuwan Annabi IBRAHIM A.S. Yazo Yana Haske Yana Kamsi Ya Duqa A Gaban Sayyida Amina A.S. Yace: “ASSALAMU ALAIKA RAHMATALLAH”.
Ya Gaishe Da Annabi S.A.W. Yayi Ma Sayida Amina A.S. Bishara da cewa: “Haqiqa Kin Sami Cikin Annabi Mai Girma”.
Annabi Ya Amsa masa ya sanya masa Albarka.
WATA NA BAKWAI Watan Al~Muharram Zuwan Annabi Isma'il A.S. Shima Yazo da kakkyawan Fuska Yana Haske Ya Gaida Annabi S.A.W. Yace: “ASSALAMU ALAIKA YA MANIKHTARAHULLAH”.
Yace Nine Annabi Isma’il A.S. Nazo in gaida shugaba kuma Inyi miki Bishara cewa: “Kin Sami cikin Ma’abocin Falala Ingantacce”.
Annabi S.A.W. Ya Amsa Kuma Ya Sanya Masa Albarka.
WATA NA TAKWAS Watan Safar ANNABI MUSA A.S.
Yayi Sallama Yana Gaida Annabi Yana cewa: "ASSALAMU ALAIKA YA HIRATULLAH". Yace mata Nine Annabin Allah Annabi Musa A.S. Nazo ne Domin In Miki Bishara cewa: “Hakika Kin Sami Cikin Wanda Allah Zai Bashi Alqur’ani Mai Girma".
"LA'ILAHA ILLALLAH" SAURA WATA DAYA ANNABI S.A.W. YA ZO DUNIYA A SHARI'A KENAN.
WATA NA TARA WATAN RABI’UL AWWAL Zuwan ANNABI ISAH A.S. {Rahillahi}. Ku sani Fa A Wannan Wata ne Daren Sha Biyu Ga Wata Daren Litini Annabi Muhammadu S.A.W. Ya Sauka A Duniya.
Sayyida Amina A.S. Taga Wannan Bako Yazo Yana Haske Yana Qamshi. Ya duqa yace: “ASSALAMU ALAIKA YA RASULALLAH”.
Yace mata Nazo ne inyi maki Bishara domin kin sami cikin “Annabin Allah abin karramawa abin Girmamawa”.
Annabi Muhammadu S.A.W. Yasanya Masa Albarka Tun Yana Ciki.
Kaji Dai Yadda Ake Neman Fada A Wajen Annabi Muhammadu S.A.W.
Don Allah Idan Ka Karanta Wannan Kayi Salatil Fatihi Kafa Daya Ga Annabi S.A.W.
ALLAHUMMA SALLI ALA SAYYIDINA MUHAMMADIN WA ALA ALIHI HAQQA QADRIHI WA MIQDARIHIL AZEE.

BISHARORI NA ZUWAN ANNABI MUHAMMADU S.A.W. DAGA MANYAN BOKAYEN YAHUDAWA.
A Garin Yamama akwai wasu Manyan Bokaye Wadanda a lokacin indai Bokanci ne babu kamarsu a duniya, Kuma Dukansu sunyi Bayanin Zuwan Annabi S.A.W. Da Sufofinsa fiye da Tinaninka, Ga Bayanin Daya Daga Cikin Bokayen.
BOKA NA FARKO SUNANSA SADIHU:- Wannan Sadihun Babban Boka ne Masanin Taurari awannan Lokacin, Shi wani Irin Halitta ne domin bashi da Hannu Bashi Da Kafa, daga Kai Sai Jiki: Dakko shi akeyi a kwanon kaya, Amma Sai Ilimi.
Wata Rana Ya Fito da daddare Yana Duba Taurari, Sai Yaga Sun Hargitse(Sai Ya Gane cewa Lallai Ba Lafiya ba) domin Yasan cewa Hakan Kawai zai iya Faruwa ne idan Har an sami cikin Annabin Karshen Zamani, Domin Shine zai zo da Addinin Musulunci zai hana Bokanci.
Sai Ya Rubuta Wasika Zuwa ga babbar Boka Ta Mace Wacce itama a duniya babu kamarta wajen ilimin Taurari da Bokanci Sunanta Zarqa’u (Bayanin ta zai zo a rubutu na gaba da izinin Allah).
Yace mata: “Lallai yaga Taurari sun rikice, kuma wannan yana nuna Alamar Bayyanan wannan Annabin Mai hallaka kafirai, mai dusashe duk addinan karya, wanda zai Zubar da jinane na kafirai Annabin Karshen Zamani, Kuma Na Tabbatar Zai Bayyana Ne a Garin Makka, Nima daga Nan Garin Makka Zan tafi domin in Tabbatar da hakan Mu Hadu dake A can”.
Aka Daukeshi zuwa Garin Makka, Yayita Bayanin Sufofin Annabi S.A.W. Kuma Har Ya Nuna Ma Mutanen Makka Cewa Ga Mahaifiyar Annabi S.A.W. Da Mahifiyar Sayyiduna Aliyu.
Banu Abdu Munafin Sunata Farin ciki domin acikin su ne, Amma Yahudawa Sukayi Bakin ciki da jin Wannan Labari.
Sadihu Ya Sami Kwanaki A Garin Makka Yana Basu Bayanin Sufofin Annabi Muhammadu S.A.W.
Abin Nufi Anan Shine Fassarar Ayannar Na cikin Suratul Bakara da Allah Yake cewa:
ﻳﻌﺮﻓﻮﻣﻪ ﻛﻤﺎ ﻳﻌﺮﻓﻮﻥ ﺍﺑﻨﺎﺀﻫﻢ
Cewa su Yahudawan nan Sun San Annabi S.A.W. Kamar Yadda Suka san 'Ya'yan Cikinsu, wasu ma sun sanshi fiye da 'Ya'yan cikinsu” amma duka bai sanya Sunyi Imani ba.
Akwai Cikakken Bayanin da Kisaa na “SADIHU” A karatun Da Maulana Sheikh Usman Kusfa Zaria R.A. Yayi Na Tarihin Annabi S.A.W. (04).

BISHARAR HAIHUWAR ANNABI MUHAMMADU S.A.W.
BOKANYA ZARQA’U.
Bayan Kaji Bayanin Da Boka Sadihu Yayi Akan Haihuwar Annabi S.A.W. Yau Kuma Zamuyi Bayanin Boka Ta Biyu Sunanta "ZARQA’U".
Wacannan Bokanya ce, Ta Kasance a garin Yaman, Duk Wanda Zai Zo wajenta Ta Kanga abinda yake zuciyarsa kafin yazo da Kwana Uku.
Itama Tazo Garin Makka Domin Ta Tabbatar da Irin Wadannan Alamomi da Ta Gani Na Bayyanar Annabi Muhammadu S.A.W.
Amma Ita ta bayyana Qiyayyarta ga Annabi S.A.W. A fili.
Domin tun a lokacin ta Hada kai da su Abu Jahil domin Ganin sun Kashe Sayyida Amina (WAI AGANINSU KADA ANNABI S.A.W. YA BAYYANA YA HANASU BOKANCI DA SAMUN KUDI HANNUN MUTANE).
Ta Sami Wata Mata Mai Kiso Ta Bata Wani Wuka Mai dafi, idan taje Zatayi ma Sayyida Amina Kitso Sai Ta Caka Mata.
Bayan Taje Gidan Sayyida Amina An Fara Kitso Sai Ta ciro Wukar Ta, Daga nan Sai Allah Ya Turo Da Wuta Ta Konata, Kaga Allah Ya Kiyaye Masoyinsa.

DAREN HAIHUWAR ANNABI MUHAMMADU S.A.W. DAREN FARIN CIKI.
INA MASOYA ANNABI MUHAMMADU S.A.W. KUZO MUTAYA JUNA MURNA DA FARIN CIKI.
Sayyida Amina A.S. Tace: "A Wannan Daren aka yaye mata Hijabai Gabas da Yamma Kudu da Arewa Tana Hango Ko Ina".
Can Sai Ta Hango Wata mata tana Haske ga Kwarjin Ta Nufo Dakinta Tana Haske Tace mata Itace Sayyida Hawwa'u Matar Annabi Adamu A.S.
Sai Ga Zuwan Sayyida Saratu Matar Annabi Ibrahim A.S.
Sai Ga Zuwan Sayyida Asiya Bintu Muzahimin.
Sai Ga Zuwan Sayyida Maryam Mahaifiyar Annabi Isa A.S.
Dukansu sunzo tare da Mala’iku Fiye da Dubu Saba’in Sun zo Rakiya.
Sukace Munzo ne Domin Mu debe maki kewa, Domin Gidan Babu Kowa Sai Ita Kadai.
Sayyida Amina A.S. Tana Kwance Ko Alamar Ciwo Bataji ba sai Farin ciki, Wadannan Matayen Suna yi mata Tausa.
Can Kuma A waje Kawai Sai Mutanen Garin Makka Sunata Jin Muryoyi Daban Daban, Garin Makka ya Cika Da Haske.
Mala'iku Sunata Farin ciki.
Dabbobin gida Sunata Farin ciki.
Dabbobin Daji Sunata Farin ciki.
Tsuntsaye Sunata Murna da farin ciki.
Suna Cewa: "MARHABAN BIKA YA MUHAMMADU, MARHABAN BIKA YA MUHAMMADU.
Sayyida Amina A.S. Tana Kwance Sai Taji Bacci ya kamata sai Taga Wani Mala’ika Yana Haske Ya Sanya Fuffukensa Ya Shafa Cikinta Sai Cikin Ya Bude Ta Wajen Cibiya.
SHUGABAN DUNIYA DA LAHIRA ANNABI MUHAMMADU S.A.W. YASA KAFARSA TA DAMA YA FITO.
ALLAHU AKBAR.
YANA SAKKOWA YA SANYA GOSHINSA A QASA YA DAGA YATSARSA SAMA YANA CEWA: "SUBHANA RABBIYAL A'ALA WA BIHAMDIHI, SUBHANA RABBIYAL A'ALA WABIHAMDIHI, SUBHANA RABBIYAL A'ALA WABIHAMDIHI, LA'ILAHA ILLALLAH QUDDUSUN QUDDUSUN, ALLAHU AKBAR KABEERAN WALHAMDULILLAHI KASIRAN WA SUBHANALLAHI BUKRATAN WA ASILAH".
ANAN ALLAH YA FARA BAYYANAR MASA SUKA GANA TUN KAFIN YA GANA DA WANI HALITTA ALLAH YACE MASA : “ ﺑﻪ ﺑﻪ ﺑﻪ ” MADALLAH, MADALLAH, MADALLAH, DOMIN YAU ANNABINA YA KARBI MABUDAN TASKAR DUNIYA DA LAHIRA BURINA YA CIKA INJI ALLAH AZZA WAJALLA.
Annabi S.A.W. Yazo A wanke babu Kazanta, A Tare da Kaya Na Gidan Aljanna, har da Tozali da Kaciyarsa domin Babu Wanda Ya Isa Yaga Al’aurar Shugaba S.A.W. Yana Haske Yana Kamshi.
LA'ILAHA ILLALLAH MUHAMMADUR RASULILLAHI S.A.W.

YAHUDAWA SUNYI NIYYAR SU KASHE ANNABI MUHAMMADU S.A.W.
Lokacin da Su Sayyida Halima Suka Kama Hanya Daga Makka Zuwa Kauyensu Jakin Ya Kara Lafiya Da Karfi da Gudu Har Ya zamto Yana Wuce Masu Doki.
Su Kuma Yahudawa Sun Taru Suna mitin akan cewa sunji labarin an haifi Annabin Karshen Zamani, Wata Hanya Zasu bi domin Su Kasheshi tun kafin Ya Girma Suna cikin wannan taron Kawai sai ga Sayyida Halima Sunzo Wucewa, Sai Shedan Ya Bayyana Masu Yace Ku Kuna Mitin to ai gashi can Zai wuce Ku bishi Sun Taso Sun biyosu Saura kadan Su Kamosu Sai Allah Ya Turo Da Wuta Gaba Daya Ya Rufesu Ya Kona Su.
Daga Nan Sayyida Halima Ta Kara Gane Darajar Wanda Ta Dakko Yahudawa Baza su iya ja Da Annabi S.A.W.

WATA MATA KAFIRA DA TAZO DA NIYYAR KASHE ANNABI MUHAMMADU S.A.W. LOKACIN HAIHUWA.
Annabi Muhammadu S.A.W.
Lokacin da Kafirai suka Sami Labarin HAIHUWAR Annabi Muhammadu S.A.W. Sai Suka Dauki Hayar Wata Mata Da Sunan Anguwan Zoma Da Niyyar Idan Taje Sai Ta Kashe Annabi S.A.W. Wai Su huta.
Da Ta Shigo Dakin Su Annabi S.A.W. A Matsayin Haihuwar Yau Kawai Sai Annabi S.A.W. Yayi Mata Wani Kallo Take Nan Ta Fadi Ta suma aka Fita Da Ita.
Da Ta Koma Wajen Kafirai Sai Tace masu Batayi tinanin zata Rayu ba, Sabida Wannan Abin Da aka Haifa Kallo Daya Yayi Mata Ta Suma, Sabida Haka Su Hakura Kawai Bazasu Iya Ja Dashiba.
Tun Daga Wannan Ranar Kafiran Makka Suka Fara Adawa da Annabi S.A.W.
Amma Allah Bai Yarda Ko Kadan Sun Cutar Da Annabi S.A.W. Ba Har Yau.


ABI LAHABIN YA ‘YANTA SAYYIDA SUWAIBA SABIDA BISHARAR DA TAYI MASA N HAIHUWAR ANNABI MUHAMMADU S.A.W.
Lokacin da aka haifi Annabi S.A.W. Sayyida Suwaiba ta kasance baiwace Ta Abi Lahabin Dan Uwan Mahaifin Annabi S.A.W.
Su Larabawa sun kasance sunaso ace an haifa masu ‘ya’ya Maza.
Da Taji Labarin Sayyida Amina A.S. Ta Haifi ‘Da Na Miji Sai Tayi Sauri Zuwa Wajen Mai gidanta Abi Lahab Ta Bashi Labarin Matan Dan Uwansa Ta Haifi ‘Da Namiji.
Da Yaji Haka Yace: "Indai Dagaske ne Na ‘Yantaki, Anan Sayyida Suwaiba Ta Zamo 'Ya.
Ko Kasan Sirrin Yin Hakan Sabida Annabi S.A.W. Cikakken Mutum ne baya Karbar Tawaya, Kuma Allah Ya Kaddara Zaisha Nononta Sabida Haka Bazaisha Nonon Baiwa Ba.
Sabida Wannan Farin cikin Da Abi Lahab Yayi Na An haifa masu ‘Da Namiji, Kuma Daga Ranar Bai Kara son Annabi Ba, Amma duk Ranar Litini Ana Saukaka Masa Azaba.
To Yaya Kuma Wanda Ya Kasance Baida Abin So Sai Annabi Muhammadu S.A.W. Matukar Rayuwarsa?.

FARIN CIKIN MALA’IKA MIKA’ILU A.S.
A lokacin Da Aka Haifi Annabi Muhammadu S.A.W. Manyan Mala’iku Guda Hudu Sunyi Bisharori Ta Bangon Dakin Ka’aba.
Na Biyu Shine Mala’ika Mika’ilu A.S. Ta Bangon Dakin Ka’aba Na Yamma Yana Cewa:
ﻗﺪ ﺟﺎﺀﻛﻢ ﻣﻦ ﺍﻟﻠﻪ ﻧﻮﺭ ﻭﻛﺘﺎﺏ ﻣﺒﻴﻦ
"Haqiqa Yaku Mutanen Duniya Haske Yazo Maku Daga Allah Ubangiji Tare Littafi Mai Yin Bayani Filla~Filla (Wato Alqur’ani)".

BISHARAR MALA'IKA ISRAFEEL A.S.
Mala’ika Israfilu A.S. Shine Mala’ika Na Uku Ta Bangaren Kudancin Dakin Ka'aba Cikin Mala’ikun da Sukayi ta Bishara agarin Makka Suna Farin ciki Da Allah Ya Bamu Annabi Muhammadu S.A.W.
Yana Biya: "LAQAD JA AKUM RASULUN Zuwa Karshe".


BISHARAR MALA’IKA AZRA'EELU A.S.
Mala'ika Azra’eelu A.S. Shine Mala’ika Na Hudu Wanda Yake Bishara Da Haihuwar Annabi Muhammadu S.A.W. Ta Bangon Dakin Ka’aba Ta Arewa.
Yana Fari ciki Yana Fadi Yana Cewa Da BABBAR Murya:
ﻭﻗﻞ ﺟﺎﺀ ﺍﻟﺤﻖ ﻭﺯﻫﻖ ﺍﻟﺒﺎﻃﻞ ﺇﻥ ﺍﻟﺒﺎﻃﻞ ﻛﺎﻥ ﺯﻫﻮﻗﺎ
"HAQIQA GASKIYA TAZO, QARYA TA WATSE, DAMA ITA QARYA WATSATSTSIYACE".


MURNAR MALA’IKU A DAKIN KA'ABA.
Lokacin Da aka Haifi Annabi Muhammadu S.A.W. Sai Mutanen Garin Makka Sukayi ta Jin Muryar Mala'iku Ta Sasannin Dakin Ka’aba.
Malaika Jibrilu A.S. Ta Gabas Yana Cewa:
ﻭﻟﺪ ﺍﻟﻤﺨﺘﺎﺭ ﺍﻟﺬﻱ ﻳﻬﻠﻚ ﺑﻴﺪﻩ ﺍﻟﻜﻔﺎﺭ ﻭﻳﻄﻬﺮﻧﻲ ﻣﻦ ﻫﺬﺍ
ﺍﻷﺻﻨﺎﻡ ﻭﻳﺄﻣﺮ ﺑﻌﺒﺎﺩﺓ ﺍﻟﻤﻠﻚ ﺍﻟﺠﺒﺎﺭ
“HAQIQA AN HAIFI ANNABI MUHAMMADU S.A.W. ZABABBEN ALLAH WANDA ALLAH ZAI HALLAKA GUMAKA SABIDA SHI, KUMA ZAI TSARKAKEMU DAGA BAUTAN GUMAKA, KUMA ZAI BADA UMURNI DA A BAUTAMA ALLAH ALJABBARU".
Wannan Shine Bisharar Mala'ika Jibrilu A.S. Ga Mutanen Duniya.

MANYAN MATAN DA SUKA SHAYAR DA ANNABI MUHAMMADU S.A.W. {Su Tara Ne}.
Ta Farko: Mahaifiyarsa Wato SAYYIDA AMINA A.S. Itace ta fara Shayar dashi Na Tsawon Kwana Bakwai.
Ta BIYU: SAYYIDA SUWAIBA itama ta shayar dashi kuma Ta Shayar da Sayyidina Hamza R.A.

TA UKU: SAYYIDA UMMU AIMANA
ita ma ta shayar dashi S.A.W.


TA HUDU: SAYYIDA HALIMATUS SA'ADIYYA (Zamu Kawo Bayanin Zamansa wajen Sayyida Halima Insha Allah A Rubutu Na Gaba).
Sannan Akwai Mata Guda Biyar a Garin Halimatus Sa’adiyya da Suka Shayar dashi Domin Neman Tubarrakinsa Kuma Sun Samu SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM.

TAFIYAR MATAN BANI SA’ADIN ZUWA GARIN MAKKA DOMIN NEMAN ABIN SHAYARWA.
Bayan Sunji Muryar Hatifi a Gona, suka shirya kowa ta hau doki lafiyayye domin zuwa garin makka.
Ita Kuwa Sayyida Halima Talaka ce, bata da Doki sai Jaki Bashi Da Gudu kuma Shedan Yaje ya shafeshi ya nakasa shi (wai da niyyarsa na hanata zuwa garin makka, amma Allah Bai bashi Iko ba).
Duka Sauran Matan Sun rigata shiga Garin Makka.
Idan Sukaje gidan su Annabi S.A.W. A kace masu wannan Maraya ne sai su Tafi wai Su bazasu Dauki Maraya ba, (Sabida Basu aka Kaddara ma ba).
Ita Kuma Sayyida Halima Ta Gama zagawa Duk Bata Sami Wani Abin Shayarwa ba, Sai Allah Ya Hadata Da Shaibatul Hamdi (Wato Abdul Mudallib).
Yace mata wannan ‘Da Maraya ne amma zanyi masa abinda ko Babansa {MAHAIFINSA} nada rai sai dai haka.
Sai Ya Tambayeta Wane sunanki? Sai Tace HalimaTussa’adiyyaI Sai Yace Ga Hakuri ga Sa’adah lallai aciki akwai alhairan duniya da Lahira.
Shaibatul Hamdi Ya Tafi da Ita Zuwa Gida Domin Ta Dauki Annabi Muhammadu S.A.W.

SAYYIDA HALIMATU ASSA'ADIYYA.
Lokacin da Allah Ya Kaddara cewa za’a kai Annabi S.A.W. Wajen Shayarwa.
Wata Rana Sai Tayi Mafarki Taji ana ce mata Lallai akwai wani abun haihuwa a garin makka, duk matar da Ta Shayar dashi Nono Arziki na duniya da Lahira Ya Tabbata A Gareta.
A cikin Baccin Sai Taga An Bata Wani Ruwa ance tasha, Sannan Aka Ce mata Ta Biya Kalamar Shahada {LA'ILAHA ILLALLAHU MUHAMMADU RASULILLAHI S.A.W.}.
Sai Tace Menene Kalmar Shahada?.
Aka ce mata tace: “LA'ILAHA ILLALLAH MUHAMMADUR RASULULLAH". Sai Aka ce mata wannan Shine Kalmar Shahada Yanzu kece farkon Musulunta, Kuma Allah Ya Zabeki Za’a Baki Shayarwar Annabin Karshen Zamani.
Kaji Wallahi Sai da Aka Musuluntar da ita Sannan Allah Ya Bata Daman Shayar Da Shugaba S.A.W.
Domin Shi Mai Tsarki ne kuma Bazaisha Nonon Wata Ba Sai Mai Tsarki.
Da Izinin Allah Akwai Cigaba A Rubutu Nagaba.

GARIN SU HALIMATUSSA'ADIYYA.
Bayan Sayyida Halima Tayi Wancan Mafarkin Da Mukayi Bayani a rubutu na Baya.
Da Safe Tayi Sai Matan Garin Suka Tafi Bayan Gari Kiwo Sai Sukaji Muryan Hatifi Daga Sama Yana Cewa: “Haqiqa An Haifi Wani Abun Haihuwa A Garin Makka, Aljannar Allah Ya Tabbata Ga Dukkan Matar da Ta Shayar dashi”.
Da Sukaji Wannan Bisharar Sai Duka Suka Dawo Gida Suka Fadama Mazajensu.
Kowa tayi Shiri da Niyyar Zuwa Garin Makka domin Samun Shayarda wannan Babban Arziki.
Suka Kama Hanya Zuwa Garin Makka.

FARKON HADUWAR ANNABI S.A.W. DA SAYYIDA HALIMA.
Sayyiduna Shaibatul Hamdi Ya shigo Da Halima Cikin Gida, Tana Shigowa Dakin Sayyida Amina A.S. Sai Taga Wani Haske Yana Tashi FAL, FAL Tare Da Kamshi sai tace: "Aminatu Da Rana Kuma Kina Kunna Fitilla? Sai Sayyida Amina Tace Wallahi Tunda Na Haifeshi Ban Taba Kunna Fitilla ba (Annabi Muhammadu S.A.W.).
Sayyida Halima Tana Daukarsa Kawai Sai Taga Ya Kalleta Yana Mata Murmushi SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM.
Tayi Farin ciki Da Samun Wannan Alhairi ta tabbatar da cewa itace Allah Yayi ma Baiwa Da Samun Wannan Alhairi.

ZUWAN ANNABI MUHAMMADU S.A.W. GARIN BANI SA’ADIN.
Bani Sa’adin Kauye ne wanda Basu Da Kayan Ni’ima, ga Talauci ba Wadata, Ga Fari Basu Da Ruwa, Dabbobinsu duk sun Kwanjame.
Amma Daga Ranar Da Annabi S.A.W. Ya Sauka Garin Suka Fara Samun Ruwa Da Abinci, Wadata Ya Karu da Ni’ima a garin.
Ita Kuwa Sayyida Halima Dabbobinta suka Kara Lafiya Sukayita Albarka Sabida Shugaban Masu Albarka ANNABI MUHAMMADU S.A.W.


TAFIYAR SAYYIDA HALIMA DA ANNABI MUHAMMADU S.A.W. ZUWA GARIN BANI SA’ADIN.
Bayan Sayyida Halima Ta amince zata dauki Annabi S.A.W. Sayyidina Abdul Mudallib Ya Bata Kudi Da Kaya Na alfarma wanda masu iyayen ma Basu sami hakan ba.
Daman Tazo ne tare da Mijinta, Sai Ta Goya Annabi S.A.W. A Baya zasu hau Jaki, Sai Wannan Jakin Yaki Tafiya, sukayi, sukayi ya tafi yaki, Sai Allah ya bashi iko yayi magana yace: "Ai indai Kunaso Inyi Tafiya To Ku Dawo Dashi Gaba! Sai Ta Dakko Annabi S.A.W. Suka sanyashi a gaba Sannan Jakinnan Yayi Farin ciki Yayi Murna Yau Gashi Shine Ya Fara Daukar Annabi S.A.W. A Bayansa.
Wannan Jaki Ya More.

ZUWAN SAYYIDA HALIMA WAJEN WANI BABBAN MALAMIN YAHUDAWA A KASUWAR UKKAZ.
Kasuwar Ukkaz Tana Kasancewa a shekara sau Daya inda Mutane Suke zuwa daga kasashen duniya don Kasuwanci.
Ita Sayyida Halimatus saadiyya Taje da Annabi S.A.W. Wannan Kasuwa Sai Taga Wani Babban Malamin Yahudawa Masanin Taurari Sai Taje Wajenshi Domin Yayi Mata Bincike Game da Wannan yaro da Take Tare dashi Ta Ba Malamin Labarin duk abinda Ta Gani Na Ban Mamaki Game dashi.
Sai Yace Ta Kawo Annabi S.A.W. Ya Ganshi, Yana Karbarshi Sai Ya Kama Ihu Yana Cewa Ya Ku Yahudawa Kuzo Ga Wanda Kuke Nema, Domin Idan Kuka Barshi Ya Girma Zai Bata Addininku kuma Zai Kasheku .
Sayyida Halima Allah Ya Taimaketa Ta Dakeshi Ta Dauki Annabi S.A.W. Ta Goya Ta Danna Da
Gudu Ta Bar Wajen.
Allah Ya Kiyayeta Daga Sharrinsu Dama Shi Annabi S.A.W. Tun Tuni Allah Ya Kiyayeshi.


SAYYIDA HALIMA TAYI KUKAN RASHIN GANIN ANNABI MUHAMMADU S.A.W.
Ranar da Sayyida Halima Ta Nemi Annabi S.A.W. Bata Ganshi ba akace Mata Wasu Mutane suka Daukeshi, Sai Tana Ihu Tana cewa: "Wayyo Ina Tausaya masa Gashi Shi Kadai Ne". A lokacin Yana Tare da Mala'ika Jibrilu A.S. Da Mika’ilu A.S.
Sai Sukace masa: "YA RASULALLAH KAJI TANA CEWA KAI KADAI NE, AI KAI DUK INDA KAKE BAKA TAFIYA KAI KADAI KANATARE DA ALLAH DA JIBRILU DA MIKA'ILU DA ISRAFILU DA AZARA'EELU TARE DA MALA'IKU DUBU SABA’IN".
Sayyida Halima Ta Kara Cewa: "Wayyo Ina Tausaya Masa Gashi Shi Maraya ne!! Sai Jibrilu A.S. Yace: "Lallai kai maraya ne domin mahaifinka Ya Rasu, Amma Kai maraya ne mai goya masu iyaye".
Sayyida Halima Ta kara cewa: "Wayyo Ina tausaya masa gashi yaro ne mai rauni" Sai Jibriliu A.S. Yace: "Ai Allah Ya baka Karfin halittun Sammai da kassai gaba daya, ai kaine sadaukin sadaukai kaine jarumin jarumai Ya Rasulallah….


AN BUDE KIRJIN ANNABI MUHAMMADU S.A.W. AN CIKATA DA HASKE.
A Rana Ta Uku Annabi S.A.W. Ya Bukaci Ya Kara Fita Wajen Kiwo Tare Da 'Yan Uwansa.
Bayan Sun Tafi Da Kamar Azahar Sai 'Yan Uwansa Duka Suka Dawo Gida Da Gudu Suna Cewa: "Halima Gashi Can Wasu Manyan Mutane Sun Kama Danki Sun Hau Dashi Saman Dutse".
Hankalin Sayyida Halima Ya Tashi Da Sauran Mutane Garin suka fito da makamai.
Wadannan Mutane Da Suka Daukeshi suka Hau Saman Dutse dashi Ashe Mala’iku ne, Mala’ika Jibrilu A.S. Da Mala’ika Mika’il A.S. Kuma Allah Ne Ya Turosu, Su Bude Kirjin Annabi Muhammadu S.A.W. Su Kara Cikata Da Haske.

GIRMA NA SHEKARU AMMA IRIN NA ANNABI MUHAMMADU S.A.W.
Girman Shekaru Na Annabi Muhammadu S.A.W.
Ya Kasance a duk sati Yana Kara Girma Na Wata Guda.
A duk wata Yana Kara Girma Na Shekara Guda.
Sannan Allah Ya Halicci Hankalin Annabi Muhammadu S.A.W. Aka kasata adadin Qura Na Duniya Sannan aka Dauki Kwaya Daya itace aka Raba ma Halittun Duniya Gaba Daya SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM.

FITAR ANNABI MUHAMMADU S.A.W. KIWO NA FARKO A GARIN SU SAYYIDA HALIMA.
Wata Rana Annabi S.A.W. Ya Tambayi Sayyida Halima Cewa: "Ina Yan Uwansa suke zuwa baya ganinsu da Rana? Sai Tace Suna zuwa Kiwo ne", Sai Yace: "Gobe Zai Bisu", Sayyida Halima Tace Bata Yarda ba Sabida Tana TSORON Yahudawa Kada Su Ganshi su cutar Dashi. Sai Yace Shidai Yanaso Yaje. Da Gobe Tayi Sai aka Shiryashi akan zai Bisu Sije Kiwo, aka Rakasu Suka Tafi.
Da Yamma Tayi Kamar La’asar Sun hanyar Dawowa Sai Annabi S.A.W. Yaji Suna Cewa a sami Magani a shafa ma Wata Akuya Da Ta Karye a kafa, Annabi S.A.W. Yace a Kawo akuyar Yace: "BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM" Ya Shafi Kafar Nata Yana Shafa Kafar Ta Warke Wannan Mu'ujizar ta Faru tun Baikai shekara hudu ba.
Sauran Yara da manya sunata Mamaki Suka Kara Tabbatar Da Darajar Annabi Muhammadu S.A.W.
Bayan Sun dawo gida Labari ya Yadu kowa sai ya kawo dabbansa da baida lafiya, Yana Shafansu Sai Su Warke SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM.


FITAR ANNABI MUHAMMADU S.A.W. KIWO NA BIYU (YAYI ZANCE DA ZAKI).
Rana Na Biyu Annabi S.A.W. Ya Kara Cewa Yana So Ya Fita Yaje Kiwo, Sayyida Halima da Sauran Mutane Sukayi Masu Adawo Lafiya.
Bayan Sun Tafi Can Wajen La’asar Sai akaga Yara Sun Dawo Da Gudu Gida Suna Cewa Gashi can Zaki Ya Kama MUHAMMADU Hankali Ya Tashi, Sayyida Halima tanata Kuka Duk Ta Damu, Mutanen Garin Kowa Ya Dakko Makami Da Niyyar Aje Dajin A Kashe Wannan Zakin Kuma A Karbo Annabi S.A.W.
Lokacin Da Sukazo Wajen Zakin, Sai Sukaga Sabanin Hankalinsu, Domin Sunga Zakin Ya Kwanta A Gaban Annabi S.A.W. Yana Ka’da Bindi Suna Fira Da Annabi MUHAMMADU S.A.W.
Sai Annabi S.A.W Ya Kallesu Yace mauu: "KADA KU TADA HANKALINKU DOMIN ZAKIN YANA FADAMIN CEWA YAZO WUCEWANE ZAIJE YA GAIDA DAN UWANSA AWANI DAJI, KUMA NA FADA MASA KADA YA KARA BIYOWA TA WANNAN GARIN DOMIN ANAN NE DABBOBINMU SUKEYIN KIWO”. SAI ZAKIN YACE: "NAJI NA YARDA YA SHUGABA NA A GAFARCENI" Sai Annabi Yace: “Jeka Allah Yayi Maka Albarka”
Mutanen Gari Sukazo Sukayita Rungume Annabi S.A.W. Suna Neman Albarkarsa.

Make a free website with Yola